Da duminsa: IGP ya sauyawa manyan 'yan sandan kudu maso gabas wurin aiki

Da duminsa: IGP ya sauyawa manyan 'yan sandan kudu maso gabas wurin aiki

- Usman Baba Alkali, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya sauyawa manyan 'yan sandan yankin kudu wurin aiki

- Sauyin wurin aikin ya shafin kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra da wasu mataimakan kwamishinonin 'yan sanda 16

- Hakan na zuwa ne yayi da ake tsaka da hargitsi tare da tarzoma a jihohin yankunan kudu maso gabas na kasar nan

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sauyawa manyan jami'an 'yan sandan yankin kudu maso gabas wurin aiki a matsayin hanyar shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya ya sanar da wannan cigaban a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, The Cable ta ruwaito.

Daga cikin wadanda aka sauyawa wurin aikin akwai Monday Bala Kuryas, kwamishinan 'yan sanda na jihar Anambra.

KU KARANTA: Sunaye: Dubun 'yan bindigan11 dake basaja a matsayin makiyaya a Oyo ta cika

Da duminsa: IGP ya kwashe manyan 'yan sandan kudu maso gabas ana tsaka da matsalar tsaro
Da duminsa: IGP ya kwashe manyan 'yan sandan kudu maso gabas ana tsaka da matsalar tsaro
Asali: Original

KU KARANTA: Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa

Mataimakan kwamishinonin 'yan sanda 16 lamarin ya shafa kuma hakan ya gangara har zuwa jihohin kudu kudu na kasar nan.

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya jaddada cewa rundunar sojin kasa ta mayar da hankali wurin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

A yayin jawabi ga manema labarai a jihar Borno a ranar Alhamis, yace ya je duba Rundunar Operation Lafiya Dole ne dake Maidguri domin ziyartar sojojin da suka samu raunika.

A yayin tabbatar da cewa dakarun sun mayar da hankali wurin shawo kan matsalar tsaro kamar 'yan bindiga da satar mutane, daga cikin miyagun al'amuran da kasar nan ke fuskanta, Attahiru yace babu yadda za a yi dakarun su ce sun samu nasara ta karya kamar yadda wasu suke zarginsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel