Jami'an Kwastam Sun Kai Samame Wata Kasuwa a Ibadan, Sun Ƙwace Buhunan Shinkafa

Jami'an Kwastam Sun Kai Samame Wata Kasuwa a Ibadan, Sun Ƙwace Buhunan Shinkafa

- Jami'an hukumar kwastam sun dira kasuwar Oja Oba dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda suka yi awon gaba da buhunan shinkafa

- Kakakin hukumar kwastam ɗin na Sakta A, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace baisan adadin buhunan da aka ƙwato ba

- Yace dokar hukumar su ta baiwa jami'ai damar ɓalle kowane irin shago ko babban ɗakin ajiye kaya matuƙar akwai sahihin bayani cewa an ajiye haramtattun kaya a cikinsa.

Jami'an hukumar kula da shige da ficen kaya (NCS) sun dira kasuwar Oja Oba dake Ibadan da sanyin safiyar ranar Asabar inda suka yi awon gaba da motar ɗaukan kaya maƙare da buhunan shinkafa yar ƙasar waje.

KARANTA ANAN: Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta gano cewa jami'an sun ɓalla shaguna da babban ɗakin aje kaya a cikin kasuwar kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wannan na zuwa ne wata ɗaya bayan jami'an sun kai irin wannan samamen a kasuwar Bodija, inda a wancan lokacin suka yi awon gaba da buhunan shinkafa.

Jami'an Kwastam Sun Dira Wata Kasuwa a Ibadan, Sun Ƙwace Buhunan Shinkafa
Jami'an Kwastam Sun Dira Wata Kasuwa a Ibadan, Sun Ƙwace Buhunan Shinkafa Hoto: infoguidenigeria.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar kwastam na sakta A, Mr Theophilus Duniya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da akai dashi ta wayar salula.

Theophilus Duniya, ya bayyana cewa aikin su ya basu ikon ɓalle kowane shago ko babban ɗakin aje kaya matukar suna zargin an ajiye haramtattun kaya a ciki.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

Yace: "Kwarai mun gudanar da aiki a wannan kasuwar, amma bazan iya faɗa muku adadin buhunan shinkafar da muka kama ba a yanzun haka."

"A iya abinda nasani, bayan gudanar da irin wannan aikin, ana ƙirga yawan buhunan shinkafar da aka kamo. Amma a yanzun da nike magana bazan iya faɗa muku sakamakon wannan aikin ba, tabbas jami'an mu sunje wannan kasuwar kuma sun kwato shinkafa."

"A dokokin hukumar mu NCS, an ba jami'ai damar su ɓalle kowanne shago ko babban ɗakin aje kaya matuƙar suna da sahihin bayanai cewa an ajiye haramtattun kaya a cikinsa."

A wani labarin kuma Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan na gudanar da wa'azin su, suna kira ga mutanen da suka rage a garin da su karɓi da'awarsu ta tsattsauran ra'ayin Jihadi.

Wata Majiya ta ƙara da cewa Yan Boko Haram ɗin sun ƙwace iko da gonaki har sun fara shirin yin noma a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel