Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa

Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa

- Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana dalilin da yasa hukumar su ta buɗe cibiyoyin maguɗin jarabawa.

- Yace sun yi haka ne domin ɗana tarko ga ɗaliban da suke da shirin yin maguɗi, da zarar sun kama mutum zasu koreshi

- Oloyede yayi kira ga cibiyoyin dake gudanar da rijista da kada su kusƙura su amshi kuɗin aikinsu ya wuce N700, duk cibiyar da aka kama tayi haka to ta kuka da kanta

Shugaban hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, yace hukumar na da cibiyoyin maguɗin jarabawar JAMB din.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Oloyede ya bayyana haka ne yayin da yake duba yadda rijistar jarabawar ke gudana a jihar Lagos, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Yace hukumar ta ƙirƙiri cibiyoyin maguɗin ne domin ta ɗana tarko ga ɗalibai masu yin maguɗi kuma ta hana su zana jarabawar.

Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa
Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Yace: "Mun cafke wasu iyaye da suka biya wani mutum kuɗi domin ya zanawa ɗansu jarabawa. Mun kore su a lokacin da muka kama su."

"Domin ka kama ɗan damfara, kana buƙatar kaima ka zama kamar shi."

"Mun buɗe cibiyoyin dake maguɗin jarabawa, inda muke cewa ɗalibai su biya N15,000 idan suna so a ƙara musu sakamakon su ya kai yadda ake buƙata. Da zarar sun bada lambar jarabawarsu zamu amshi kuɗin kuma mu hana su yin jarabawar."

Shugaban JAMB ɗin ya kuma yi Allah wadai da makarantun dake amsar sama da N4,700 domin siya da kuma yin rijistar jarabawar ga ɗalibansu.

KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leƙen asiri

Oloyede ya gargaɗi duk wani mai son yin jarabawar ta bana da kada ya kuskura ya biya sama da N4,700 domin siya da kuma yin rijista.

Ya kara jaddada cewa duk cibiyar da aka kama tana amsar sama da N700 kuɗin rijista to za'a hana ta aikin gaba ɗaya.

Yace: "JAMB na amsar N3,500 amma mafi yawancin makarantu na amsar abinda yafi haka. Mun sanar da ma'aikatar ilimi, kuma zan sake sanar dasu domin su ɗau mataki kan waɗannan makarantun."

"Shugaban ƙasa ya rage kuɗin jarabawar zuwa N3,500, sai kuma kuɗin littafi N500, da kuɗin yin rijista da zaka biya N700. Zamu kulle duk wata cibiyar CBT da muka kama tana amsar sama da N700."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel