APC Za Ta Kai Ƙarar Mbaka Wurin Fafaroma Saboda Yi Wa Buhari Barazana

APC Za Ta Kai Ƙarar Mbaka Wurin Fafaroma Saboda Yi Wa Buhari Barazana

- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta gargadi Fada Ejike Mbaka kan kalamansa na cewa Buhari ya yi murabus

- Yekini Nabena, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce zai yi karar Mbaka wurin Fafaroma Francis

- Nabena ya shawarci Mbaka ya yi koyi da sauran malaman addinin kirista kaman Enoch Adeboye wurin yi wa kasa addu'a

Yekini Nabena, mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya ce Ejike Mbaka, Shugaban cocin Adoration Ministry, Enugu, (AMEN) yana yi wa gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari barazana, The Cable ta ruwaito.

Nabena ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke martani kan kalaman da aka ce babban malamin addinin kiristan ya yi.

DUBA WANNAN: 2023: An Ƙaddamar da Ƙungiyar Goyon Bayan Saraki a Daura

APC Za Ta Kai Ƙarar Mbaka Wurin Fafaroma Saboda Yi Wa Buhari Barazana
APC Za Ta Kai Ƙarar Mbaka Wurin Fafaroma Saboda Yi Wa Buhari Barazana. Hoto: @thecableng
Asali: Instagram

A wa'azinsa na ranar Laraba, Mbaka ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus saboda tabarbarewar tsaro a sassa Nigeria.

A jawabinsa a ranar Juma'a, jigon na APC ya ce idan Mbaka ya cigaba da furta kalaman da za su 'janyo mutane su dena bin dokokin kasa', zai yi kararsa wurin Fafaroma Francis, shugaban cocin Katolika na duniya.

KU KARANTA: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

Nabena ya ce kamata ya yi Mbaka ya rika addu'o'i da fatan samun zaman lafiya amma yana yin barazana ga gwamnatin demokradiyya saboda wasu bukatun kansa yayin da ya ke fakewa da sunan magana a madadin mutane.

Ya bukaci Mbaka ya yi koyi da Enoch Adeboye na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) wanda ya mayar da hankali wurin addu'o'i da azumi domin ganin kasar ta magance matsalolin da ta ke fama da su.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel