Matasa Sun Ƙona Motocci da Gidajen Mai Garkuwa da Mutane a Kwara
- Wasu fusatattun matasa sun kona dukiyar wanda ake zargi da garkuwa da mutane
- Mutumin wanda ake zargi sun hada kai da wani abokin sa, sun shiga komar sojoji
- Matasa a yankin da abun ya faru a jihar Kwara na ci gaba da farautar mutanen biyu
Wasu fusatattun matasa, ranar Juma'a, sun kona wasu kadarori mallakin wani Romoni, da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, a Omu-Aran, a karamar hukumar Irepodun da ke Jihar Kwara.
Wasu daga cikin kayayyakin da matasan suka kona sun hada da motoci guda biyu, gidaje guda biyu, da kuma wani ginin Otal mallakin wanda ake zargin dan garkuwar ne, rahoton The Cable.
DUBA WANNAN: Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina
Romoni, wanda aka ruwaito cewa sojoji yi awon gaba da shi tare da wani Bunmi Popoola, da aka ce abokin harkar sa ne, bisa zargin su da hannu a garkuwa da mutane a Odo-Owa, karamar hukumar Oke-Ero da ke jihar ranar Alhamis.
Kamar yadda NAN, wani mafarauci da ba a bayyana sunan sa ba a Odo-Owa ne ya shaidawa jami'an tsaro suka kuma dakatar da biyan kudin fansar wanda aka yi garkuwar da shi.
Wasu daga cikin masu garkuwar sun tsere daga inda abun ya faru, yayin da Romani, wanda ke mota tare da Bunmi ke tunkarar inda abun ya faru, inda anan sojoji suka kama su.
KU KARANTA: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC
Popoola, mai shekaru 27, yana daya daga cikin yan majalisar sarki a Odo-Owa wanda an kore shi a watan Oktobar 2016 saboda zargin aikata miyagun laifuka.
An ruwaito cewa matasan yankin na farautar mutanen biyu.
A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.
Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.
Asali: Legit.ng