Hotunan Taron Majalisar Tsaro da Buhari Ya Yi da Shugabannin Tsaro a Aso Rock

Hotunan Taron Majalisar Tsaro da Buhari Ya Yi da Shugabannin Tsaro a Aso Rock

- Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar taron kwamitin tsaro na kasa a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja

- Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ma ya halarci taron

- Baya ga shugabannin tsaron, wasu daga cikin ministoci da manyan ma'aikatan fadar shugaban kasa sun halarci taron

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana nan yana jagorantar taron majalisar tsaro a fadar Shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Sai Shugaban Ma'aikatan Fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, NSA Manja Janar Babagana Monguno (mai murabus) da kuma wasu ministoci.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai

Hotunan Taron Majalisar Tsaro da Buhari Ya Yi da Shugabannin Tsaro a Aso Rock
Hotunan Taron Majalisar Tsaro da Buhari Ya Yi da Shugabannin Tsaro a Aso Rock Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Shugabannin sojoji da suka halarci taron sun hada da, Manjo Janar Lucky Irabor; Babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Babban hafsan sojojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amoo; da babban hafsan sojojin ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Sauran sun hada da sufeta janar na yan sanda Usman Alkali, Shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi da shugaban NIA, Ahmed Rufai Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Kashe-Kashe: Daga Karshe Tinubu Ya Yi Magana, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Yan Najeriya

A gefe guda, mai girma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwaransa na jihar Kebbi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu, sun zauna da shugaban ‘yan sanda na kasa.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnonin biyu sun yi zama da mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Baba da nufin shawo kan matsalar tsaro.

Dr. Kayode Fayemi shi ne shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, a yayin da Atiku Abubakar Bagudu ya ke rike da kujerar shugaban gwamnonin jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel