Tsaron kasa: Buhari ya fusata, yace Ortom baya ganin laifin kansa, na wasu yake hange
- Fada shugaban kasa tace Buhari ya matukar fusata da kalaman Gwamna Samuel Ortom
- Buhari yace dama laifi ai tudu ne, Samuel Ortom yana take nasa inda yake hango na wasu
- Gwamna Ortom ya zargi Buhari da goyawa Fulani baya a kasar nan inda suke cin karensu babu babbaka
Fadar shugaban kasa tayi martani kan zargin da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi a kan matsalar tsaro.
Ortom a ranar Talata ya zargi shugaban kasa Buhari da yi wa Fulani aiki domin su karbe Najeriya a martanin da yayi kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa wanda ake zargin makiyaya ne.
Amma kuma mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Malam Garbe Shehu, ya kushe ikirarin Gwamna Ortom.
KU KARANTA: Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3
A wata takarda mai take 'Gwamna ortom matsalar wasu kawai yake hangowa, baya hangen tasa,' wacce Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ya ce shugaban kasa ya matukar damuwa da kashe-kashen da ake yi tare da ikirarin gwamnan.
Ya ce, "Shugaban kasa ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda aka rasa a kashe-kashen kwanan nan a jihar Binuwai.
"Bugu da kari, yace karuwar miyagun al'amuran ballantana kashe-kashe da fada a yankunan kasar nan yana bukatar hadin kan dukkan hukumomin tsaro domin hana cigaban faruwar lamurran.
“Ya kara da bayyana fushinsa tare da kunyar da kalaman Samuel Ortom, Gwamnan jihar Binuwai suka bashi inda ya zargi shugaban kasan da gwamnatinsa bayan mummunan abinda ya faru a jiharsa."
A wani labari na daban, dakarun sojin Kamaru a ranar Litinin, 26 ga watan Afirilu sun fatattaki wasu mayakan Boko Haram da suka kai farmaki garin Wulgo na jihar Borno dake yankin arewa maso gabas, babu nisa da tsakaninsu da Fotokol dake yankin arewacin Kamaru, kakakin rundunar yace.
Kamar yadda takardar da aka fitar a ranar Laraba, 28 ga wata Afirilu ta bayyana, Kyaftin Atonfack Gueno Cyrille Serge, shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Kamaru, yace 'yan Najeriya dake Wulgo sun samu tsaro daga dakarun Kamaru yayin da Boko Haram suka kai musu farmaki.
Aikin ya samu shugabancin sashi na daya na MNJTF dake tafkin Chadi, kuma an kai harin ne a yammacin Litinin.
Asali: Legit.ng