Ta'addanci: Mun mayar da hankali wurin ganin bayan Boko Haram, COAS

Ta'addanci: Mun mayar da hankali wurin ganin bayan Boko Haram, COAS

- Shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Attahiru ya jaddada cewa sun mayar da hankali wurin yaki da Boko Haram

- Kamar yadda ya sanar da manema labarai, babu yadda za a yi su dinga ikirarin nasara bayan basu sameta ba kamar yadda ake zarginsu

- Ya isar da fatan alherin Buhari ga dakarun tare da tabbatar musu da cewa shugaban ya mayar da hankali wurin samar musu da kayan aiki

Shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya jaddada cewa rundunar sojin kasa ta mayar da hankali wurin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

A yayin jawabi ga manema labarai a jihar Borno a ranar Alhamis, yace ya je duba Rundunar Operation Lafiya Dole ne dake Maidguri domin ziyartar sojojin da suka samu raunika.

A yayin tabbatar da cewa dakarun sun mayar da hankali wurin shawo kan matsalar tsaro kamar 'yan bindiga da satar mutane, daga cikin miyagun al'amuran da kasar nan ke fuskanta, Attahiru yace babu yadda za a yi dakarun su ce sun samu nasara ta karya kamar yadda wasu suke zarginsu.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan

Ta'addanci: Mun mayar da hankali wurin ganin bayan Boko Haram, COAS
Ta'addanci: Mun mayar da hankali wurin ganin bayan Boko Haram, COAS. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5

"Mun mayar da hankali sosai kan aikinmu ta yadda muke fatan ganin bayan Boko Haram a Najeriya," yace.

“Dakarun sun shirya kawo karshen yakin da sauran matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan kamar garkuwa da mutane."

Shugaban sojin kasan ya mika fatan alkhairin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma kwamandan sojojin kasar nan ga dakarun, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda yace, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali wurin samar da duk abinda ake bukata na yaki da ta'addanci tare da duk wasu kungiyoyin tada zaune tsaye a fadin kasar nan.

A wani labari na daban, a ranar Talata, 27 ga watan Afirilun 2020, 'yan daba a jihar Sokoto sun kone ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Kware ta jihar.

Gungun 'yan daban da suka kunshi matasa, sun isa ofishin 'yan sandan inda suka dinga ihu tare da jaddda cewa akwai wasu wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane amma aka sake su.

'Yan daban sun fi karfin 'yan sandan inda suka rinjayi jami'an tsaron dake gadin ofishin kuma suka koneshi tare da motar DPO da kuma motocin sintiri guda biyu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel