Kada ku sassautawa 'yan bindiga, Matawalle ya sanar da alkalai

Kada ku sassautawa 'yan bindiga, Matawalle ya sanar da alkalai

- Gwamnan jihar Zamfara, yayi kira ga alkalai a jihar da kada su yi sassauci ga 'yan bindiga yayin da suke shari'arsu

- Ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin wasu mahukunta tare da ma'aikatan shari'a a gidansa domin yin buda baki

- Gwamnan yace yana bukatar alkalan su yi shari'ar cike da kishin kasa kuma ba tare da sassauci ba ga miyagu

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi kira ga alkalai a jihar da kada su kasance masu sassauci ga 'yan bindiga yayin shari'a.

Kamar yadda The Punch ta wallafa, Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin da ya karba wasu mahukunta da ma'aikatan bangaren shari'a na jihar buda baki a gidansa dake Gusau.

"Ina kira ga alkalan dake shari'ar 'yan bindiga da su yi shari'ar cike da kishin kasa kuma ba tare da wani sassauci domin kawo karshen wannan matsalar a jihar."

KU KARANTA: Sunaye: Dubun 'yan bindigan11 dake basaja a matsayin makiyaya a Oyo ta cika

Kada ku sassautawa 'yan bindiga, Matawalle ya sanar da alkalai
Kada ku sassautawa 'yan bindiga, Matawalle ya sanar da alkalai. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye

Gwamnan ya sanar da ma'aikatan shari'ar cewa gwamnatinsa ta samar da sabbin ababen hawa da za ta baiwa alkalan kotun majistare da na shari'ah a jihar.

Gwamnan ya jinjinawa ma'aikatan shari'ar a kan yadda suke aiki tare da tabbatar da alaka mai kyau tsakaninsu da masu mukamin siyasa a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta samu manyan nasarori sakamakon goyon baya da hadin kan da take samu ballantana a matsalalolin da kai tsaye suka shafi jama'ar jihar.

A yayin jawabi a madadin masu buda baki, kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru magarya, ya jinjinawa gwamnan a kan yadda yake hada kai dasu a abubuwan da suka shafi jihar saboda hadin kai da cigaban Zamfara.

A wani labari na daban, dan majalisa mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa da Garara ta jihar Neja a majalisar wakilai, Rt Hon Abubakar Lado Suleja, ya farantawa 'yan mazabarsa rai.

Suleja ya ziyarci mazabarsa inda ya raba kudi har naira miliyan 50 ga jama'a albarkacin wannan wata na Ramadan.

An tattaro hakan ne a wata wallafa da wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Victor Kelechi Onyendi yayi tare da hotunan rabon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng