Muhimmiyar Sanarwan da CBN ta baiwa ma'aikatanta ya tada hankalin mazauna Abuja

Muhimmiyar Sanarwan da CBN ta baiwa ma'aikatanta ya tada hankalin mazauna Abuja

- Sanarwar da babban bankin Najeriya ta fitarwa ma'aikatan ya tashi hankulan mazauna garin Abuja

- Babban bankin Najeriya ya bukaci ma'aikatansa da su gujewa tafiye-tafiye, yin dare a waje, rayuwar almubazzaranci da sauransu

- Hukumar tsaro ta babban bankin ta fitar da hakan inda tace tana gujewa kutsowar miyagu Abuja, amma hakan ya tada hankula

Mazauna babban birnin tarayya suna cikin tashin hankali bayan sanarwar tsaro da babban bankin kasar nan ya baiwa dukkan ma'aikatanta dake fadin kasar nan.

An fitar da takardar ne a ranar Laraba ta hannun hukumar tsaro na babban bankin Najeriyan (CBN).

Wasu ma'aikatan babban bankin da suka zanta da jaridar Daily Trust da sharadin za a boye sunansu, sun tabbatar da ingancin takardar.

Takardar ta bukaci dukkan ma'aikatan bankin da su daina tafiye-tafiye barkatai, yin dare a waje, rayuwar almubazaranci da zata janyo hankalin 'yan ta'adda har su kutsa babban birnin tarayyan.

KU KARANTA: Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye

Sanarwan da CBN ta baiwa ma'aikatanta a kan tsaro ya tada hankalin mazauna Abuja
Sanarwan da CBN ta baiwa ma'aikatanta a kan tsaro ya tada hankalin mazauna Abuja. Hoto daga @daily_trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a

Wata mazauniya garin mai suna Nanman Philemon tace: "Yadda tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar nan abun damuwa ne, bai taba kai haka ba. Wannan hauhawar rashin tsaron ya shafi ma'aikata masu tarin yawa.

"Ni ma'aikaciyar jinya ce kuma an sace wasu daga cikin abookan aikina. A makon da ya gabata ne aka sace wasu ma'aikatan jinya biyu a Kaduna kuma an kashe wata daya a jihar Abia har gidanta aka bi ta.

"Yayin da matsalar tsaro ta shafi kowa, ina kira ga gwamnati da ta shawo kan matsalar tsaro gaba dayanta," tace.

A wani labari na daban, shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya jaddada cewa rundunar sojin kasa ta mayar da hankali wurin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

A yayin jawabi ga manema labarai a jihar Borno a ranar Alhamis, yace ya je duba Rundunar Operation Lafiya Dole ne dake Maidguri domin ziyartar sojojin da suka samu raunika.

A yayin tabbatar da cewa dakarun sun mayar da hankali wurin shawo kan matsalar tsaro kamar 'yan bindiga da satar mutane, daga cikin miyagun al'amuran da kasar nan ke fuskanta, Attahiru yace babu yadda za a yi dakarun su ce suna samu nasara ta karya kamar yadda wasu suke zarginsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel