Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye

Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye

- Zakakuran sojin kasar Kamaru sun ragargaji 'yan Boko Haram da suka kai hari kauyen Wulgo dake Borno

- Kamar yadda takardar da rundunar ta bayyana, sun sakarwa 'yan ta'addan ruwan wuta inda suka kwace miyagun makamai

- Rundunar tace tana shirye a halin yanzu koda wasu 'yan ta'addan zasu sake kai mugun farmakin

Dakarun sojin Kamaru a ranar Litinin, 26 ga watan Afirilu sun fatattaki wasu mayakan Boko Haram da suka kai farmaki garin Wulgo na jihar Borno dake yankin arewa maso gabas, babu nisa da tsakaninsu da Fotokol dake yankin arewacin Kamaru, kakakin rundunar yace.

Kamar yadda takardar da aka fitar a ranar Laraba, 28 ga wata Afirilu ta bayyana, Kyaftin Atonfack Gueno Cyrille Serge, shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Kamaru, yace 'yan Najeriya dake Wulgo sun samu tsaro daga dakarun Kamaru yayin da Boko Haram suka kai musu farmaki.

Aikin ya samu shugabancin sashi na daya na MNJTF dake tafkin Chadi, kuma an kai harin ne a yammacin Litinin.

KU KARANTA: Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya

Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye
Sojojin Kamaru sun kaiwa 'yan Najeriya dauki, sun sheke 'yan Boko Haram a wani kauye. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

Takardar ta bayyana cewa, "Bayan arangamar, 'yan ta'addan sun sauya hanya kuma an kwace makamansu masu yawa."

Babu wanda MNJTF ta rasa yayin da suke kashe 'yan ta'addan, ta lalata motocin 'yan ta'addan shida tare da kwace wasu miyagun makamansu.

Kakakin rundunar sojin ya bayyana cewa dakarun har yanzu suna ankare domin fuskantar kowanne irin salon hari da zai iya zuwa musu.

HumAngle ta ruwaito cewa, dakarun sojin Najeriya sun fattataki mayakan ISWAP da na Boko Haram a ranar Litinin, 26 ga watan Afirilu wanda suka tsinkayi Wulgo da garin Gwoza dake yankin arewa maso gabas ta kasar nan.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

A wani labari na daban, Opeyemi Bamidele, sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, yace bashi da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da tsaron kasar nan ke fuskanta.

Bamidele ya sanar da hakan a ranar Talata a tsakar majalisar dattawa yayin bada gudumawa a kan wata bukata da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas ya bijiro da ita.

Musa ya janyo hankalin majalisar a kan rahoton na kafa tutocin da Boko Haram suka yi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, The Cable ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel