Sunaye: Dubun 'yan bindigan11 dake basaja a matsayin makiyaya a Oyo ta cika
- Jami'an rundunar tsaro ta jihar Oyo ta damke wasu 'yan bindiga 11 da ke basaja a matsayin makiyaya
- 'Yan bindigan suna saka shinge ba bisa ka'ida ba akan tituna da dare inda suke tare fasinjoji tare da yi musu fashi tare da sacesu
- Sunayen 'yan bindigan shine: Awali Atine, Ibrahim Abu, Shuaib Balau, Ibrahim Musa, Abdullah Masika da Umar Aliu Masika
Jami'an rundunar tsaro na jihar Oyo a ranar Alhamis, 29 ga watan Afirilu, sun damke wasu makiyaya 11 a kan hannunsu dumu-dumu cikin garkuwa da mutane a jihar.
Kamar yadda kwamandan OSSNA, Kanal Olayinka Olayanju ya sanar, shida daga cikin 'yan bindigan an kama su ne a karamar hukumar Kajola ta jihar yayin da sauran biyar aka kama su a karamar hukumar Saki ta gabas bayan sun saka shinge a titi.
Olayanju cewa yayi: "An kama su ne a wuri mabanbanta inda suke aikata laifi bayan saka shingen kan titi ba bisa ka'ida ba da suka yi.
KU KARANTA: Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3
"Sun yi kokarin tserewa daga wurin amma jami'an tsaro sun bi su kuma sun kama su.
"Muna cigaba da neman sauran da suka tsere. Sunayen 'yan bindigan da aka kama shine: Awali Atine, Ibrahim Abu, Shuaib Balau, Ibrahim Musa, Abdullah Masika da Umar Aliu Masika."
Ya ce 'yan bindigan sun samo sabon salo na yin basaja a matsayin makiyaya da rana kuma suna kaiwa fasinjoji farmaki a manyan hanyoyi da dare.
Ya kara da cewa an samu shanu 183, kudi N268,470 da kuma miyagun makamai daga hannunsu, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
Kwamandan ya bayyana cewa dukkan wadanda ake zargin za a mika su ga hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya dake Okeho.
A wani labari na daban, Sanata Clifford Ordia yayi kira a kan garambawul a fannin tsarin tsaron kasar nan bayan 'yan bindiga sun kai masa farmaki har sau biyu a cikin sa'o'i 24 a wata tafiya da yayi.
'Yan bindigan sun kaiwa sanatan mai wakiltar Edo ta tsakiya farmaki har sau biyu a ranar Litinin a kan babban titin Okene zuwa Lokoja da kuma titin Lokoja zuwa Abuja, Daily Trust ta wallafa.
Ordia wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattawan a harkokin bashin cikin gida da waje, ya sanar da manema labarai a garin Abuja cewa an sakarwa tawagarsa ruwan wuta yayin da yake komawa Abuja daga garinsu na Edo.
Asali: Legit.ng