Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan

Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan

- Babban malamin addinin Islman, Sheikh Dahiru Bauchi, ya koka da yadda rashin tsaro ke kamari a kasar nan

- Ya ce 'yan Najeriya basu taba tsammanin hakan zata faru ba a karkashin wannan gwamnatin

- Malamin yace 'yan Najeriya yanzu zaman dar-dar suke yi a gidajensu, a kan tituna da kuma gonakinsu

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan, inda yace babu wanda ta tsallake.

Babban malamin yace hakkin gwamnati ne kare 'yan kasa daga 'yan bindiga da sauran miyagun da suka addabesu, Daily Trust ta wallafa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan tsokacin ne bayan karbar wakilan Kiristoci da yayi wanda suka samu jagorancin tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung da kuma Fasto Yohana Buru na Peace Revical and Reconciliation of Nigeria dake gidansa na Kaduna a ranar Talata.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan
Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Bani da tabbacin Buhari ya san halin da kasa ke ciki, Sanatan APC

Malamin ya kwatanta yanayin rashin tsaron kasar nan da abun damuwa, inda ya kara da cewa 'yan Najeriya basu taba tsammanin hakan zata faru ba a zamanin wannan gwamnatin.

"Abinda muke tsammani daga dukkan matakan gwamnati na tarayya, jiha da karamar hukuma shine mafita ta yadda kowa zai zauna hankali kwance.

“Hatta a cikin gida zaman dar-dar ake yi, a kan titi ba a tsira ba, kuma gwamnati bata wanke mana wannan tsoron ba.

“Bamu zabesu domin mu kasance a wannan halin ba, bamu zabesu domin su siyar damu kamar dabbobi ba ko kuma su dinga mana duk yadda suka so. Abinda ke faruwa tabbas abun damuwa ne.

"Mun san gwamnati ta san abinda ke faruwa a kasar nan, mun san gwamnoninmu sun sani kuma kananan hukumomi sun sani.

"Don haka, su sauraremu saboda bama iya zuwa gona saboda tsabar tsoro. Gwamnati tayi abinda ya dace ta hanyar baiwa 'yan kasa Musulmi da Kirita kariya daga miyagu," yace.

A jawabinsa, dalung yace sun ziyarci malamin ne domin yin buda baki tare da yi wa kasa Najeriya addu'a.

A wani labari na daban, bayan miyagun hare-haren da 'yan Boko Haram suka kai a garin Geidam dake jihar Yobe a ranar Juma'a, 23 ga watan Afirilu, sun raba wasika ga mazauna yankin yayin harin.

A yayin bada dalilin da yasa suke kaiwa 'yan Najeriya hari, kungiyar 'yan ta'addan a wasikar ta bayyana cewa Boko Haram ta zo yin jihadi ne da rundunar sojin Najeriya.

A karin bayani, an rubuta wasikar a harshen Hausa kuma a wasikar an jaddada cewa sun fito ne domin halaka duk wani wanda ke hana Jihadi ko kuma yake aiki tare da hukumar tsaron Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel