Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5

Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5

- Shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya siya wani katafaren gida

- Tamfatsesen gidan yana nan a Miami inda yake kallon wata korama mai bada sha'awa dake gudana

- Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 33 ya siya gidan ne a kan kudi har pam miliyan biyar

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na cikin duhu a kan makomar Kyaftin Lionel Messi wanda kwangilarsa zata kare a karshen wannan kakar.

Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 33 ya bar kungiyarsa a watan Augustan da ya gabata.

Amma kuma, nan da watanni biyu dan kasar Argentinan zai kammala kwangilarsa kuma zai iya neman wata kungiyar ba tare da damuwar kungiyar da yake a yanzu ba.

KU KARANTA: Sunday Igboho ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki gidansa

Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5
Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5. Hoto daga Republic World
Asali: UGC

KU KARANTA: Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa

Daga Manchester City har Paris Saint Gerrmain sun nuna bukatarsu na karbar shahararren dan wasan kwallon kafan da burin cewa ba zai cigaba da zama a Nou Camp.

Amma kuma wannan tsarin kamar ba zai yuwu ba saboda rahotannin dake yawo na cewa ya siya tamfatsetsen gida mai darajar pam miliyan biyar a Miami.

Kamar yadda Republic World ta ruwaito, wannan ce kadara ta biyu da dan wasan kwallon kafan ya siya a Amurka a cikin shekarun nan.

An gano cewa Messi ya zuba kudi har pam miliyan 3.6 domin siyan katafaren gidan a Miami wanda aka gina a shekarar 2017.

Rahotanni daga The Real Deal sun yi ikirarin cewa dan wasan kwallon kafan ya siya dukkan hawa na tara na katafaren gida a garin Florida.

Kayataccen gidan yana nan a wurin wata kyakyawar bakin ruwa wanda yake kallon wata korama kuma an gano cewa ya kashe pam miliyan 5 a kan shi.

A wani labari na daban, kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno a ranar Litinin da dare.

Kamar yadda jama'a da dama suka wallafa a shafinsu na Twitter, mayakan sun isa garin wurin karfe takwas na dare kuma suka dinga sakin ruwan wuta.

Kungiyar masu tsaurin ra'ayin ta shiga garin Gwoza a ranar 26 ga watan Afirilun 2021 inda suka dinga harbe-harbe yayin da mazauna yankin suka dinga tserewa zuwa tsaunika domin neman wurin buya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: