75% na ɗaliban jami'ar Jihar Kaduna KASU zasu bar makarantar Saboda ƙarin kuɗi, ASUU
- Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jami'ar jihar Kaduna, ya bayyana cewa wannan ƙarin kuɗin zaiyi sanadiyyar barin ɗalibai da yawa daga makarantar.
- A cewarsa, ɗalibai sama da kashi 70% ka iya barin karatunsu domin iyayen su ba zasu iya biyan kuɗin ba
- Ya kuma roƙi gwamnatin jihar ta sake zama domin duba wannan ƙarin kuɗin da tayi, kuma ta gayyato masu ruwa da tsaki a fannin
Ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU, reshen jami'ar jihar Kaduna KASU, tace kashi 75% na ɗaliban makarantar ka iya barinta saboda wannan ƙarin kuɗin.
KARANTA ANAN: Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023
Shigaban ASUU, reshen jami'ar, Peter Adamu, shine ya bayyana haka ranar Laraba, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Yace wasu ɗaliban zasu bar makarantar ne saboda iyayen su ba zasu iya ɗaukar nauyin biyan wannan ƙuɗaɗen ba.
Mr. Adamu ya roƙi gwamnatin jihar da ta sake duba wannan matakin data ɗauka na ƙarin kuɗin makarantar, ta gayyato masu ruwa da tsaki a kan lamarin.
Ya ƙara da cewa ilimi dama ce ga kowa ba wai alfarma ba kamar yadda yake ƙunshe a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa, kuma aikin gwamnati ne ta samar da ilimin ba na iyayen yara ba.
Yace KASU na da ɗalibai sama da 19,000 dake karatu a cikinta, kuma sama da 17,000 daga cikinsu yan asalin jihar ne.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta
Shugaban yace sama da kashi 70% na ɗaliban da suke yan jihar 'yayane ga Manoma, ma'aikata, da kuma ƙananan yan kasuwa.
Yace: "Abun takaicin shine gwamnati ta kori ma'aikata, daga cikinsu akwai iyaye da kuma masu kula da ɗaliban mu. Waɗannan mutanen na iya ƙoƙarinsu suga sun biyawa yayansu kuɗin makaranta."
"Ƙara kuɗin makaranta da kashi 500%, babu shakka zai sa dubbannin ɗalibai subar makarantar. Wannan ƙarin zai hana ɗalibai da yawa shiga makarantar wanda hakan barazana ce ga ƙudirin gwamnati na kawo cigaba a jihar."
Shugaban ASUU, ya ƙara da cewa wannan ƙarin ƙuɗin makarantar zai sake fito da banbancin dake tsakanin mai kuɗi da Talaka.
A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.
Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'
Asali: Legit.ng