'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3

'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3

- Rundunar 'yan sandan jihar Binuwai ta sanar da artabun da suka yi da 'yan bindiga

- Kamar yadda suka sanar, 'yan sandan sun sheke uku daga cikinsu yayin da suke musayar wuta

- Anene tace sansanin 'yan bindigan na nan rufe a surkukin dajin Tomatar Imande dake Katsina-Ala

Rundunar 'yan sandan jihar Binuwai tace jami'anta sun halaka 'yan bindiga uku yayin samamen da suka kai sansaninsu a ranar Laraba.

Catherine Anene, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, tace 'yan sandan sun samu miyagun makamai kamar su AK-47, harsasai, wukake, adduna da kuma layu.

Kamar yadda takardar da kakakin 'yan sandan ta fitar ta nuna, sansanin 'yan bindigan na rufe ne a dajin Tomatar Imande dake karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar.

Rundunar tace uku daga cikin 'yan bindigan sun samu raunika yayin da suke musayar harbin bindiga da 'yan sandan amma daga baya sai suka mutu, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3
'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tashin hankali: 'Yan daba sun fi karfin 'yan sanda, sun kone ofishinsu a Sokoto

"A yayin samamen, an dade ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan sandan da 'yan bindigan," takardar tace.

"A halin yanzu, an kama 'yan bindiga uku dauke da miyagun raunika yayin da sauran suka tsere.

“Wadanda suka samu raunin an kai su asbiti amma kuma daga bisani sai suka mutu.

“Gawawwakin wadanda suka mutu suna ma'adanar gawa dake asibitin koyarwa na jihar Binuwai, dake Makurdi."

Anene tayi kira ga mazauna yankin dasu hada kai da 'yan sanda wurin samar da labarai masu amfani da zasu sa a kama wadanda suka gudun.

A wani labari na daban, jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, yace halin da tsaron kasar nan ke ciki na bukatar dubawa da tantancewa tare da samo maslaha.

Ya yadda cewa mulkin yanzu yana bukatar hadin kai da gane halin da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci, Channels TV ta ruwaito.

Tinubu ya sanar da hakan ne a daren Litinin yayin da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati tare da jigon APC, Bisi Akande, bayan taron da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel