Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarewa a Kasar, Inji Dan Majalisa Na APC

Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarewa a Kasar, Inji Dan Majalisa Na APC

- Abdulrazak Namdas, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sojoji, ya koka kan tabarbarewar lamarin tsaro a kasar

- Namdas ya ce babu isassun jami'an tsaro kama daga na rundunar soji, yan sanda da sauransu a kasar

- Ya kuma jaddada cewa majalisar dokokin kasar a shirye take ta ba Shugaba Muhammadu Buhari hadin kai don magance dumbin matsalolin tsaro a Najeriya

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sojoji, Honorabul Abdulrazak Namdas ya koka kan yadda yanayin rashin tsaro ya tabarbare a kasar, yana mai cewa abubuwa na dada lalacewa.

Da yake magana yayin wata hira a shirin gidan talabijin din Channels ta Siyasar Yau, Namdas ya koka kan rashin isassun jami’an Sojojin Najeriya, ‘Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro.

"Na yarda cewa abubuwa na dada tabarbarewa amma bari mu zauna mu sake tsara dabaru tare da ganin yadda za mu magance matsalar," in ji shi.

Duba ga yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa, majalisar a ranar 17 ga watan Maris ta kafa kwamiti na musamman don samar da mafita ga matsalolin tsaro a kasar.

Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarwewa a Kasar – Dan Majalisa
Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarwewa a Kasar – Dan Majalisa Hoto: The Whistler NG
Asali: Twitter

Kwamitin mai mutum 40 yana karkashin jagorancin Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, kuma zai kunshi dukkan Shugabannin Majalisar da sauran mambobi 30.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Kaduna Ta Ayyana Kujerar Tsohon Kakakin Majalisar Ba Kowa, Ta Tsawaita Dakatar da Wasu 4

Amma Namdas, wanda ke wakiltar Mazabar Jada / Ganye / MayoBelwa / Toungo na Jihar Adamawa, ya ce Majalisar dokoki ta kasa a shirye take ta ba Shugaba Muhammadu Buhari hadin kai don magance dumbin matsalolin tsaro a Najeriya.

Ya kara da cewa, “Ina ganin dole ne mu sauya dabaru kuma hakan ne ya sa a Majalisar Wakilai, kasancewar Shugaban Majalisar ya yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi na mutum 40 wanda shi da kansa ke shugabanta yana nufin cewa akwai kudirin siyasa.

“Wannan kudiri na siyasa ba kawai yana fitowa daga Fadar Shugaban kasa ko kuma wani bangare na gwamnati ba ne. Shugaban majalisar shine mutum na hudu a Najeriya kuma ya fahimci cewa akwai matsala kuma hakan ne yasa muke so mu zauna mu duba inda matsalolin suke.”

Da yake ci gaba da magana, dan majalisar ya dora alhakin rashin aikin yi da talauci a kan matsalolin rashin tsaro a kasar, inda ya nemi Gwamnatin Tarayya ta samar da ayyukan yi a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya.

KU KARANTA KUMA: Ta fasu: DSS ta gano jihar da 'yan IPOB ke kwasar bama-bamai suna kaiwa Imo

Ya yi bayanin cewa sojojin na gudanar da ayyuka a jihohi 34 daga cikin 36 na tarayyar, yana neman a baiwa ‘yan sanda kwarin gwiwa, a ba su karin horo don magance barazanar tsaro na cikin gida a Najeriya.

A wani labarin, garuruwan da yan bindiga suka lalata a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun tattauna da ‘yan ta’adda domin tsagaita wuta.

Wannan ya biyo bayan wata yarjejeniya da mutanen garuruwan suka yi da 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a kauyukansu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai kuma jaridar ta ce ba ta iya tantance bayanan da ke zagaye da lamarin biyan haraji ga ’yan ta’adda a garuruwan da abin ya shafa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel