Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta

Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta

- Al'umman garuruwan da yan bindiga suka addaba a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja na neman sulhu da yan ta'addan

- An tattaro cewa garuruwan sun dauki wannan mataki ne domin ganin zaman lafiya ya dawo yankinsu

- Sai dai ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton

Garuruwan da yan bindiga suka lalata a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun tattauna da ‘yan ta’adda domin tsagaita wuta.

Wannan ya biyo bayan wata yarjejeniya da mutanen garuruwan suka yi da 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a kauyukansu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai kuma jaridar ta ce ba ta iya tantance bayanan da ke zagaye da lamarin biyan haraji ga ’yan ta’adda a garuruwan da abin ya shafa ba.

Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta
Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A cewar bayanai daga karamar hukumar, mutanen sun fara tattaunawa da 'yan ta'addan, wadanda ke kai musu hari, domin samun zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Yanzu Ba Lokacin Tsige Buhari Bane, Inji Wani Sanata

A halin da ake ciki, wata majiyar ‘yan sanda, wacce ba ta son a ambace ta, ta ce sun samu labarin cewa ‘yan ta’addan sun nemi mazauna kauyen da su biya musu haraji.

Jagoran Kungiyar Matasan Shiro, Sani Abubakar Yusuf Kokki, ya ce dukkan garuruwa da kauyukan gundumar Gurmana da Manta na karamar hukumar Shiroro sun tattauna da 'yan ta'addan.

“Kusan dukkanin garuruwa da kauyuka a gundumomin Gurmana da Manta na karamar hukumar Shiroro, jihar Neja sun tattauna da ‘yan ta’adda domin tsagaita wuta bayan cimma yarjejeniyar wani adadin kudi a tsakanin wasu sharudda da suka hada da saya masu babura kirar Honda.

"Haka nan kuma, wasu garuruwa da kauyuka a cikin yankin Bassa / Kukoki sun bi sahu ta hanyar amincewa da biyan wasu kudade da sauransu yayin da 'yan ta'addar suka dakatar da ayyukansu na assha," in ji shi.

Daily Trust ta tattaro cewa wasu kauyuka suna biyan kimanin Naira miliyan 2 ban da sauran bukatun kungiyar.

Wasu mazauna yankin, wadanda suka koka kan halin kuncin da suke ciki a hannun ‘yan ta’addan, sun ce sun gwammaci su biya kudaden shigarsu a wajensu idan har za su bar su da zaman lafiya maimakon biyan gwamnatin da ba ta damu da tsaro da walwalarsu ba.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba a samu jin ta bakin sa ba a lokacin hada wannan rahoton kuma wayar sa ta hannu na a kashe.

A wani labarin, Babagana Zulum, gwamnan Borno, ya ce hakkinsa ne ya bari shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san gaskiya game da yanayin tsaro a arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21

Sama da shekaru goma, yankin na ci gaba da fuskantar hare-hare daga maharan Boko Haram.

A baya-bayan nan maharan sun kaddamar da wasu hare-hare, musamman a duk fadin garuruwan Borno, inda suka kashe mazauna garin da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel