Majalisar dokokin Kaduna Ta Ayyana Kujerar Tsohon Kakakin Majalisar Ba Kowa, Ta Tsawaita Dakatar da Wasu 4

Majalisar dokokin Kaduna Ta Ayyana Kujerar Tsohon Kakakin Majalisar Ba Kowa, Ta Tsawaita Dakatar da Wasu 4

- Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ayyana kujerar tsohon kakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali (APC, mazabar Sabon Gari) babu kowa

- Ta dauki wannan matakin ne a kan zarginsa da rashin halartan zama ko wasu harkokin Majalisar

- Sai dai kuma Shagali ya sha alwashin zuwa kotu domin a cewarsa majalisar ba ta da hurumin aikita haka tunda bai sauya sheka ba

Rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Kaduna ya dauki sabon salo a ranar Talata bayan ayyana kujerar tsohon kakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali (APC, mazabar Sabon Gari) babu kowa a kan zargin rashin halartar zama.

Majalisar, a zamanta na ranar Talata, ta lura cewa tsohon kakakin bai shiga cikin ayyukanta ba tsawon kwanaki 120 kamar yadda doka ta tanada.

'Yan majalisar sun amince da kudurin da Alhaji Ahmed Mohammed (Zariya Kewaye) ya gabatar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majalisar dokokin Kaduna Ta Ayyana Kujerar Tsohon Kakakin Majalisar Ba Kowa, Ta Tsawaita Dakatar da Wasu 4
Majalisar dokokin Kaduna Ta Ayyana Kujerar Tsohon Kakakin Majalisar Ba Kowa, Ta Tsawaita Dakatar da Wasu 4 Hoto: Nigeria Newspaper
Asali: UGC

Har ila yau majalisar ta kara wa’adin dakatar da wasu mambobinta hudu na tsawon watanni 12.

KU KARANTA KUMA: Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta

An yanke shawarar ne yayin zaman majalisar wanda Mataimakin kakakin Majalisar, Isaac Auta Zankai ya jagoranta.

Mambobi hudu da aka tsawaita dakatarwarsu sune Mukhtar Isa Hazo (mazabar Basawa), Salisu Isa (mazabar Magajin Gari), Nuhu Goro Shada Lafiya (Mazabar Kagarko) da Yusuf Liman (Mazabar Makera).

Majalisar ta umarci magatakardar da ya isar da hukuncinta a kan lamarin ga dukkan ‘yan majalisar da abin ya shafa.

Idan za a iya tunawa dai Shagali ya yi murabus ne a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar da ta gabata a matsayin kakakin majalisar, saboda dalilai na kashin kansa, abin da ya haifar da bayyanar Yusuf Zailani kakakin majalisar na yanzu.

A ranar 11 ga Yuni, an sami 'yanci ga kowa a majalisar, biyo bayan yunƙurin aiwatar da canjin shugabanci. Rikicin da ya haifar da dakatar da 'yan majalisar da abun ya shafa.

Da aka tuntube shi, Shagali ya ce majalisar ba ta da ikon bayyana kujerarsa a matsayin ba kowa, ya kara da cewa zai nemi hakkinsa ta fuskacin doka.

“Ban sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa ba kuma akwai wasu sharuda kafin a bayyana kowane kujera a matsayin ba kowa. Hujjar su ta ayyana kujera ta fanko ba zata iya tsayawa a gaban kotu ba.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Dahiru Bauchi ya magantu a kan matsalar tsaron kasar nan

“Za mu je kotu don neman hakki domin har yanzu ni dan jam’iyyar APC ne kuma yana cikin Kundin Tsarin Mulkin 1999 na kasar nan kamar yadda aka yi wa kwaskwarima cewa idan ka sauya sheka daga jam’iyyarka zuwa wata jam’iyya za a iya bayyana kujerar ka a matsayin babu kowa. Don haka a wurina, har yanzu ina cikin APC. Ba na tsammanin suna da ikon bayyana kujera ta fanko. Don haka za mu je kotu,” inji shi.

A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da cewa a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun ne za a yi zaben shekarar 2023 a kasar.

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron yini guda da aka gudanar don sauraron laifukan zabe na 2021 da kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel