Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023

Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023

- Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da ranar babban zaben shekarar 2023

- Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar na kasa ya ce ranar Asabar 18 ga watan Janairun 2023 za a yi zaben

- Farfesa Yakubu ya sanar da hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja wurin taron da Majalisar Dattawa kan INEC ta shirya

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da cewa a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun ne za a yi zaben shekarar 2023 a kasar.

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron yini guda da aka gudanar don sauraron laifukan zabe na 2021 da kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Amince a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria

Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaben Shekarar 2023
Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaben Shekarar 2023. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

A cewar shugaban na INEC, saura shekara daya da watanni tara da makonnin biyu da kwana shida ko kuma kwanaki 660 a yi zaben daga yau.

"Kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada, zaben zai kasance a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, ya rage saura shekara guda da watanni tara da sati biyu da kwanaki shida ko kwanaki 660 daga yau."

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

"Muna fatan za mu fitar da jadawalin zaben da zarar an kammala zaben gwamna na jihar Anambra wanda za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2021.

"Don yin hakan, ya dace a samu tabbaci kan tsarin dokokin zabe don gudanar da zaben. Muna fatan Majalisar Tarayya za ta yi abin da ya dace a cikin lokaci," in ji Farfesa Yakubu.

Yakubu ya ce daya daga cikin ayyukan da hukumar ke yi shine gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe, wanda ya ce shine mafi wahala a cikin ayyukan INEC.

Ya koka da cewa rashin gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe cikin lokaci shine babban kallubalen da hukumar ke fama da shi tun kafuwarta.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel