Rashin Tsaro: Yanzu Ba Lokacin Tsige Buhari Bane, Inji Wani Sanata

Rashin Tsaro: Yanzu Ba Lokacin Tsige Buhari Bane, Inji Wani Sanata

- Sanata Mohammed Sani Musa ya bayyana cewa yanzu ba lokaci ne da ya kamata a gabatar da wani kudiri na tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba

- A cewar Musa yin hakan wani rikici ne da kasar ba ta bukata a halin da ake ciki

- Ya ce yanzu kamata yayi a mayar da hankali wajen samun mafita ga lamarin tsarin tsaro a kasar

Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas, ya ce yanzu ba lokaci ba ne na gabatar da wani kudiri da ke neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Talata, 27 ga watan Afrilu, Musa ya ce tsigewar wani 'rikici ne' da kasar ba ta bukata, jaridar The Cable ta ruwaito.

Musa ya fadi haka ne bayan an tambaye shi dalilin da ya sa ‘yan majalisar ba su yi wani yunkuri na tsige Buhari daga mukaminsa ba saboda tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya.

Rashin Tsaro: Yanzu Ba Lokacin Tsige Buhari Bane, Inji Wani Sanata
Rashin Tsaro: Yanzu Ba Lokacin Tsige Buhari Bane, Inji Wani Sanata Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21

“Ni da kai mun san abin da ake nufi da tsige shi. Yana nufin wani rikici zuwa wani rikicin. Me yasa muke bukatar hakan yanzu? Abin da muke bukata shi ne mafita, ”in ji dan majalisar.

“Muna bukatar wannan kasar ta dawo yadda muke ta fuskar zaman lafiya. Zan fi son yanayin da zai zamana duk ayyukan gwamnati zai koma ga lamarin tsaro.

“Duk wani abin da za mu yi a kasar nan, ya kasance na magance matsalar rashin tsaro. Ba mu tsira ba. Babu wani shugaba, daga kansila har zuwa shugaban kasa, da zai yi bacci ido biyu rufe.

“Ban yarda da halin da za a ce saboda muna da ikon tsige shi a matsayin yan majalisa, cewa muna kawo wani kudirin tsige shi.

"Yanzu ba lokacin gabatar da kudiri game da tsige shi bane."

KU KARANTA KUMA: APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023, 'Yan Najeriya Suna Son Jam'iyyar Mai Mulki, Inji Tinubu

Sanatan ya ce baya goyon bayan yin afuwa ga masu laifi.

"Ban yarda da yin afuwa ga masu aikata laifuka da ke ci gaba da kashe mutane da sunan addini ba. Ba addini bane, ba musulunci bane," in ji shi.

A wani labarin, Babagana Zulum, gwamnan Borno, ya ce hakkinsa ne ya bari shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san gaskiya game da yanayin tsaro a arewa maso gabas.

Sama da shekaru goma, yankin na ci gaba da fuskantar hare-hare daga maharan Boko Haram.

A baya-bayan nan maharan sun kaddamar da wasu hare-hare, musamman a duk fadin garuruwan Borno, inda suka kashe mazauna garin da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel