Lokaci yayi da zamu nemi taimako, Saraki ya baiwa shugaba Buhari shawara
- Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya shawarci shugaba Buhari da ya nemi taimako daga duk inda yake tsammanin za'a taimaka masa
- Yace Najeriya na cikin wani yanayi da dole sai gwamnati ta nemi taimako domin abun yafi ƙarfinta, kuma hakan ba yana nuna gazawarta bane
- Tsohon sanatan yace 'yan Najeriya sun shiga cikin wani matsanancin hali, basu bukatar wasu kalamai ko jawabai
Tsohon shugaban majalisar dattijai, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya shawarci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da su ɗauki matakin gaggawa wajen neman taimako domin daƙile kashe-kashen dake faruwa a faɗin ƙasar nan.
KARANTA ANAN: Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram
Saraki ya bayyana hakane a wani jawabi da ya sanya wa hannu kuma aka baiwa manema labarai a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yace Najeriya ba zata manta da ranar Litinin 26 ga watan Afrilu ba saboda a ranar ne 'yan bindiga suka kai munanan hare-hare a jihohi maban-banta na ƙasar nan.
A jawabin nasa, Saraki yace:
"Shugaba Buhari da gwamnatinsa na buƙatar taimako, wannan matsalar tafi ƙarfinsu kuma tabbas suna buƙatar taimako daga kowa. Ina roƙon shugaban ƙasa ya nemo taimako a koma ina ne, yakamata ya san cewa neman taimako ba yana nuna gazawarsa bane."
KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda jirgin yaƙin NAF, Boko Haram Suka hallaka sojoji 33 a Mainok
"Ranar Litinin 26 ga watan Afrilu, Najeriya ta ɗanɗana rana mai muni da ba zata taɓa mantawa da ita ba a tarihi. A wannan ranar ne aka samu rahoton kai hare-hare a jihohin Anambra, Ƙaduna, Lagos, Yobe da Neja."
"Mun karanta rahoton cewa mayaƙan Boko Haram sun kafa tutocin su a wasu ƙauyukan jihar Neja, yankin dake ɗauke da tashar wutar lantarki mafi girma a Najeriya. Kuma kilomita 200 ne tsakaninta da Abuja."
Saraki ya kuma koka kan yadda duk wani yunƙurin gwamnati na magance matsalolin baya haifar da ɗa mai ido.
Ya ƙara da cewa yanzun a wannan lokacin da kuma yanayin da ake ciki, 'yan Najeriya basa buƙatar komai illa su ga aiki a ɓangaren tsaro.
A wani labarin kuma Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca
Wata Mata ma'aikaciyar lafiya a jihar Nasarawa ta bayyana babbar illar da rigakafin korona ta Astrazeneca ta yi mata.
Matar mai suna, Goselle Manya, ta kwanta matsanancin rashin lafiya tun bayan da aka yi mata rigakafin wadda akace wajibi ce ga ma'aikatan lafiya.
Asali: Legit.ng