Rashin tsaro: Tinubu ya gana da Buhari, yace babu shugaban kasan da zai so a gurgunta kasarsa
- Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigon jam'iyyar APC ya ziyarci shugaba Buhari a fadarsa dake Abuja
- Kamar yadda tsohon gwamnan yace, babu shugaban kasa ko mai mulki da zai zuba ido yana kallon kasarsa na gurguncewa
- Gogaggen dan siyasan ya bukaci hadin kai daga 'yan kasa ta hanyar watsi da banbancin addini ko na kabila a kasar nan
Jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, yace halin da tsaron kasar nan ke ciki na bukatar dubawa da tantancewa tare da samo maslaha.
Ya yadda cewa mulkin yanzu yana bukatar hadin kai da gane halin da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci, Channels TV ta ruwaito.
Tinubu ya sanar da hakan ne a daren Litinin yayin da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati tare da jigon APC, Bisi Akande, bayan taron da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
"Babu shugaban kasa ko mai mulkin da zai so ganin gurguncewar kasarsa saboda kabilanci, banbancin addini da sauransu kuma hakan yasa ake bukatar tantancewa a wasu lokuta," yace.
KU KARANTA: Hotunan jana'izar Mai Babban Daki, mahaifiyar Sarakuna Aminu da Nasiru Bayero
KU KARANTA: Borno: Soji sun ragargaza yaran kwamanda Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza
Kamar yadda tsohon gwamnan jihar Legas yace, hanyar da tafi dacewa ta shawo kan matsalar kasar nan shine hadin kai da zama abu daya.
Ya musanta labarin dake yawo na cewa a halin yanzu babu alaka mai kyau tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ya bada tabbacin cewa shugaban kasan zai bar ofishinsa matukar wa'adin mulkinsa ya cika.
"Kowacce kasa tana iya shiga matsanancin hali kuma yadda suke ganawa da jama'a tare da bincike shi ke sa a a samu mafita da wuri. Dole ne shugabanni su samu wannan bayani daga jama'a," Tinubu yace.
A wani labari na daban, Opeyemi Bamidele, sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, yace bashi da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da tsaron kasar nan ke fuskanta.
Bamidele ya sanar da hakan a ranar Talata a tsakar majalisar dattawa yayin bada gudumawa a kan wata bukata da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas ya bijiro da ita.
Musa ya janyo hankalin majalisar a kan rahoton na kafa tutocin da Boko Haram suka yi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, The Cable ta wallafa.
Asali: Legit.ng