Borno: Soji sun ragargaza yaran kwamanda Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza

Borno: Soji sun ragargaza yaran kwamanda Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza

- Rahotanni da suke zuwa sun nuna cewa 'yan Boko Haram sun kai hari garin Gwoza

- Sun tsinkayi garin wurin karfe 8 na daren Litinin inda suka dinga sakin ruwan harsasai

- An gano cewa dakarun soji sun halaka yaran Abou Muhammad, wani babban kwamandan Boko Haram

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno a ranar Litinin da dare.

Kamar yadda jama'a da dama suka wallafa a shafinsu na Twitter, mayakan sun isa garin wurin karfe takwas na dare kuma suka dinga sakin ruwan wuta.

Kungiyar masu tsaurin ra'ayin ta shiga garin Gwoza a ranar 26 ga watan Afirilun 2021 inda suka dinga harbe-harbe yayin da mazauna yankin suka dinga tserewa zuwa tsaunika domin neman wurin buya

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake

Bornon: Soji sun ragargaza yaran Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza
Bornon: Soji sun ragargaza yaran Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Facebook

Karamar hukumar Gwoza ce inda Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta tsakiya, Alin Ndume ya fito. Kuma shine shugaban kwamitin sojojin kasa na majalisar dattawa.

Sanata Ndume ya tabbatar da harin sannan ya sanar da cewa, "wasu miyagun 'yan ta'adda a halin yanzu suna ruwan wuta a mahaifata," ya sanar a daren.

Baya ga Sanata Ndume, ga wasu wadanda suka yi wallafa a kan harin da ke faruwa:

@YuaufAli1 cewa yayi: "Yan ta'addan Boko Haram ta bangaren Abou Muhammad #JAS a halin yanzu sun kai farmaki ga sojoji dake Gwoza. Mazauna yankin suna gudun neman tsira."

@binyaminu_24744 yace: "Rundunar sojin kasan Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin Boko Haram a garin Gwoza mai nisan kilomita kadan daga Maiduguri. Rahotanni sun nuna cewa an sheke 'yan ta'addan masu yawa yayin da kadan daga ciki suka tafi da raunika. Allah ya karawa zakakuran sojin kasar nan nasara."

@YemiOke cewa yayi: "Boko Haram a halin yanzu sun kai farmaki karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno."

KU KARANTA: IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi kuma shugaban kwamitin tuntuba na jam'iyya mai mulki ta APC, Yahaya Bello, ya ce gwamnoni masu yawa daga jam'iyyar PDP da sauran manyan jam'iyyu na kokarin komawa APC.

Wannan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi na cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya tsaf domin barin jam'iyyar PDP zuwa APC.

Yayin zantawa da manema labarai bayan taron sirri da yayi da kwamitinsa a hedkwatar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a Abuja, Gwamna Bello yace jam'iyyar adawa ta san abubuwan dake faruwa a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: