Rashin tsaro: Bani da tabbacin Buhari ya san halin da kasa ke ciki, Sanatan APC

Rashin tsaro: Bani da tabbacin Buhari ya san halin da kasa ke ciki, Sanatan APC

- Sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, Opeyemi Bamidele yace yana tantama ko shugaba Buhari ya san halin da kasar nan ke ciki

- Sanatan ya sanar da hakan ne a zauren majalisar dattawa yayin da ake tattaunawa kan Boko Haram da ta shiga jihar Neja

- Sanata Musa daga jihar Neja ya bukaci taro tsakanin Buhari, shugabanin majalisar da kuma masu ruwa da tsaki a kan tsaro

Opeyemi Bamidele, sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, yace bashi da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da tsaron kasar nan ke fuskanta.

Bamidele ya sanar da hakan a ranar Talata a tsakar majalisar dattawa yayin bada gudumawa a kan wata bukata da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas ya bijiro da ita.

Musa ya janyo hankalin majalisar a kan rahoton na kafa tutocin da Boko Haram suka yi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU

Rashin tsaro: Bani da tabbacin Buhari ya san halin da kasa ke ciki, Sanatan APC
Rashin tsaro: Bani da tabbacin Buhari ya san halin da kasa ke ciki, Sanatan APC. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fayose: Abinda ke faruwa da Pantami na bayyana munafincin gwamnatin Buhari

A yayin jawabi, dan majalisar Ekitin ya bukaci a yi taro tsakanin shugabannin majalisar, shugaban kasa da kuma masu ruwa da tsaki domin nemo maslaha a kan kalubalen tsaron da ake fuskanta.

"Bani da tabbacin cewa shugaban kasa ya san dukkan abinda ke faruwa. Kuma idan Lawan zasu gana da shugaban kasan, dukkan hafsoshin tsaro da wadanda ya dace su kasance a wurin," Bamidele yace.

An amince da shawararsa a cikin wani bangare na bukatar da Musa ya mika.

Hakazalika, Ike Ekweremadu, sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma, yace dukkan gwamnatin da ba za ta iya baiwa 'yan kasarta tsaro ba, ta rasa "darajarta".

"Dukkan gwamnati da ba zata iya baiwa 'yan kasarta kariya ba, ta rasa darajarta," Tsohon mataimakin shugaban majalisar ya sanar.

“Kada mu ji kunyar neman taimako. Lokaci yayi da Najeriya zata rufe kasarta kuma ta baiwa 'yan kasa kariya. Lokaci yayi da za a rufe majalisar dattawa kuma a nemo maslaha."

Hakalika, Matthew Urhoghide, sanata mai wakilatar Edo ta kudu, ya goyi bayan matsayar Ekweremadu, inda yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta nemi taimako wajen shawo kan matsalar tsaro.

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kaiwa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho hari a gidansa dake Soka, Ibadan a jihar Oyo.

'Yan bindigan sun kutsa gidansa kamar yadda masu magana da yawunsa, Koiki Olayomi da Dapo Salami suka sanar.

Kamar yadda suka ce, maharan sun tsinkayi gidan wurin karfe 1:30 na dare kuma sun yi yunkurin bankawa gidan wuta amma masu tsaronsa suka hana.

Duk da hadimansa basu tabbatar da cewa an yi musayar wuta ba, Vanguard ta tattaro cewa bangarorin biyu sun yi musayar wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: