Hotunan jana'izar Mai Babban Daki, mahaifiyar Sarakuna Aminu da Nasiru Bayero
- Cike da fawwala lamurran ga Allah, an yi jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano da Sarkin Bichi
- Hajiya Maryam Ado Bayero ta rasu bayan jinya a ranar Asabar a wani asibiti dake kasar Masar
- Jana'izar ta samu halartar manya daga fadar shugaban kasa, sarakuna da kuma gwamnatin Kano
An yi jana'izar uwargidan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, Hajiya Maryam Ado Bayero wacce aka fi sani da Mai Babban Daki.
Hajiya Maryam ita ce mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero kuma diya ce ga Sarkin Ilori a jihar Kwara.
Da yammacin ranar Litinin, 26 ga watan Afirilun 2021 aka yi jana'iza tare da birneta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Manyan mutane sun samu damar halartar jana'izar, daga cikinsu akwai ministoci, ma'aikatan fadar shugaban kasa da kuma jiga-jigai daga gwamnatin jihar Kano wadanda suka samu jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Hakazalika, manyan sarakunan gargajiya sun samu halartar jana'aizar.
Kamar yadda shafin masarautar Kano ya wallafa a Facebook: "Muna addu'ar Allah ya kyautata makwancinta, yasa an je a sa'a. Allah ya gafarta mata kurakurenta kuma ya bata Aljanna madaukakiya. Allah ya bada hakurin jure wannan rashi da aka yi."
KU KARANTA: Sunday Igboho ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki gidansa
Hajiya Maryam ta rasu a ranar Asabar da ta gabata ne sakamakon jinyar da tayi fama da ita a wani asibiti dake kasar Masar.
A farko, an sanar da cewa za a yi jana'izarta a ranar Lahadi da yammaci wurin karfe 4, amma kafin nan sai sahfin masarautar Kano ya sanar da cewa an dage jana'izar zuwa karfe 11 na safiyar Litinin idan Allah ya nufa.
KU KARANTA: IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari
A wani labari na daban, Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya ce cece-kuce da ake yi a kan Isah Pantami, ministan sadarwa, ya fallasa munafincin dake kunshe a mulkin shugaba Buhari.
Wasu 'yan Najeriya da kungiyoyi sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fatattaki ministan a kan tsoffin tsokacinsa a kan kungiyoyin Al-Qaeda da Taliban.
Amma a yayin martani, fadar shugaban kasa ta bakin Malam Garba Shehu, tace gwamnati tana tare da ministan, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng