Majalisar Dattijai Sun Yanke Wata Muhimmiyar Shawara Game Da Matsalar Tsaro, Zasu Gana Da Buhari

Majalisar Dattijai Sun Yanke Wata Muhimmiyar Shawara Game Da Matsalar Tsaro, Zasu Gana Da Buhari

- Majalisar dattijai ta yanke shawarar ganawa da shugaba Buhari kan ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar nan

- Yan majalisun sun yanke wannan hukunci ne bayan sun saurari kudiri daga bakin, Sanata Mohammed Sani Musa daga mazaɓar Neja ta gabas kan halin da jihar Neja ke ciki

- Kuma majalisar dattijan tayi kira ga masu ruwa da tsaki su ɗauki sabbin jami'an tsaro kuma su samarwa jami'an tsaron makaman da suke buƙata domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan

Sanatoci sun yi kira da a ɗauki sabbin jami'an tsaro cikin gaggawa kuma a samarwa dukkan jami'an tsaron da ake dasu makamai domin su cigaba da yaƙi da yan ta'adda a ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram

Hakanan kuma majalisar ta ɗora wa shuwagabannin ta alhakin ganawa da Buhari domin tattaunawa kan matsalar tsaron da ake fama dashi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Bayan haka, majalisar dattijan ta kirayi shuwagabannin tsaro da su zo su mata jawabi kan ƙoƙarin da suke yi wajen daƙile matsalar.

Daraktan hukumar fasaha (NIA) da kuma ministan harkokin kasashen waje na cikin waɗanda aka gayyata domin suyi jawabi kan yanayin da ƙasar Chadi ke ciki da kuma tasirinsa da matsalar tsaron Najeriya.

Sanatocin sun ɗauki wannan matakan ne bisa kudirin da takwaransu, Muhammed Sani Musa daga jihar Neja, ya kawo gaban majalisar kan ƙaruwar kashe-kashe da yan bindiga ke yi a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi a jihar Neja.

Majalisar Dattijai Sun Yanke Wata Muhimmiyar Shawara Game Da Matsalar Tsaro, Zasu Gana Da Buhari
Majalisar Dattijai Sun Yanke Wata Muhimmiyar Shawara Game Da Matsalar Tsaro, Zasu Gana Da Buhari Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ya tattauna da sakataren Amurka

A cikin kudirin nasa, Senator Musa yace tsawon shekaru bakwai kenan yankin da yake wakilta a jihar Neja (Neja ta gabas) na fama da hare-haren mayaƙan Boko Haram, waɗanda a koda yaushe suke ɗauke da muggan makamai.

Ya kuma bayyana cewa: "Kusan ƙauyuka 42 dake ƙarƙashin ƙananan hukumomi biyu, Shiroro da Munya, yanzun haka sun koma ƙarƙashin ikon yan Boko Haram."

"Sannan kuma mutanen dake zaune a wannan ƙauyukan kusan 5,000 sun bar gidajensu a cikin kwanaki uku da suka gabata."

"Sama da mutane 475 ne suka rasa rayuwarsu a wannan yankin tun daga watan Janairu zuwa yanzun."

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari

Daraktan ƙungiyar magoya bayan Bola Tinubu , Aminu Sulaiman ya bayyana dalilin da yasa yan arewa zasu fi son Tinubu ya gaji shugaba Buhari a zaɓe mai zuwa.

Ya ce jagoran APC ɗin yayi sadaukarwa mai yawa a baya kuma yana da duk wani abu da ake buƙata na jagorancin wannan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel