Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe

Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe

- Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai ƙarkashin jagorancin kwamishinan Ilimin jihar suje su yiwa iyayen ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka kashe ta'aziyya

- A jawabinsa na wajen ta'aziyyar, kwamishinan Ilimin, Shehu Muhammed, yace gwamnati na nan akan bakarta na babu tattaunawar sulhu tsakaninta da yan bindiga

- A kwanakin baya dai wasu yan bindiga suka kai hari jami'ar Greenfield dake jihar Ƙaduna inda suka yi awon gaba da wasu ɗalibai

Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai zuwa gidan iyayen ɗaliban Greenfield da aka kashe domin yi musu ta'aziyya kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara

Wakilan waɗanda kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Muhammed, ya jagoranta sun ziyarci iyalan mamatan a Jaji dake Barnawa, sabon Tasha dake Igabi da kuma ƙaramar hukumar Chikun.

A yayin da kwamishinan ke jawabin ta'aziyya ga iyayen waɗanda aka kashe ɗin, ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta fara ƙoƙarin ƙara tsaro a kewayen makarantar.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin ta fara duba yuwuwar ɗauke ɗalibai daga makarantun dake wajen gari zuwa wurin da take ganin yafi tsaro.

Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe
Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe Hoto: voanews.com
Asali: UGC

Kwamishinan ya ƙara jaddada matsayar gwamnatin na ba zata yi tattaunawar sulhu da yan bindiga ba duk kuwa da matsanancin rashin tsaron da ake ciki a jihar.

KARANTA ANAN: NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok

A jawabinsa, kwamishinan yace:

"Hakanan wani mutum ya ɗauki makami a kan ɗan uwansa ɗan ƙasa, wannan ya saɓawa kundin tsarin mulki, kuma ba zamu amince da hakan ba, gwamnan mu bazai taɓa yarda da haka ba."

Ɗaliban da aka kashe ɗin dai suna aji na uku ne a karatunsu, suna karantar tattalin kuɗi kafin a sace su kuma a kashe su.

An sace ɗaliban ne a makon daya gabata ranar Talata, kuma jami'an tsaro sun gano gawarwakinsu ranar Jumu'a a wani ƙauye dake kusa da makarantarsu.

A wani labarin kuma Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

Sanatan yace bai kamata ana nuƙu-nuƙu a lamarin su ba, kamata yayi a gudanar da binciken su a fili

Ndume ya ƙara da cewa rashin tsaro a ƙasar nan yakai inda yakai, domin bazai ba kowa shawa'ar zuwa ko ina a cikin Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel