Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari
- Daraktanp ƙungiyar magoya bayan Bola Tinubu, Aminu Sulaiman ya bayyana dalilin da yasa yan arewa zasu fi son Tinubu ya gaji shugaba Buhari a zaɓe mai zuwa
- Ya ce jagoran APC ɗin yayi sadaukarwa mai yawa a baya kuma yana da duk wani abu da ake buƙata na jagorancin wannan ƙasar
- A cewarsa yadda jama'ar jihar Kano suka nuna amincewar su ga takarar Bola Tinubu, wannan babbar alama ce yan arewa gaba ɗaya zasu amince dashi domin Kano itace zuciyar Arewa
Daraktan ƙungiyar magoya bayan Bola Tinubu (TSO), Aminu Sulaiman, yace yan arewa zasu fi son jagoran APC ɗin ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023 dake tafe.
KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda jirgin yaƙin NAF, Boko Haram Suka hallaka sojoji 33 a Mainok
Sulaiman ya bayyana haka ne a wani taro da ƙungiyar ta gudanar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Yace jagoran jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu, yayi sadaukarwa da yawa kuma yana da duk wani abu da ake buƙata na jagorancin ƙasar nan.
A jawabin Mr. Sulaiman ɗin yace yan arewa sun amshi Tinubu yadda yakamata, inda yace:
"Taron da Tinubu ya gudanar a jihar Kano ya nuna yadda mutanen arewa suka amshe shi hannu biyu. Idan aka yarda da mutum a Kano, wadda itace zuciyar arewa, hakan na nufin gaba daya arewa sun yarda da shi."
"Matuƙar jama'ar Kano suka amince da kai, to tabbas jama'ar jigawa, Kaduna, Katsina da sauran jihohin arewa zasu amince da kai."
KARANTA ANAN: Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca
Sulaiman ya kuma yi iƙirarin cewa baza'a haɗa tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da jagoran APC, Bola Tinubu ba matuƙar dukkan su suka nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
"Ko dan saboda damar da Tinubu ya baiwa Atiku da Ribaɗo suka tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyyar da yake da iko (2015), hakan ya ƙara tabbatar da shi jagora ne nagari. Yan arewa basu shirya ƙara zaɓen Atiku ba a wannan lokacin." inji shi.
A wani labarin kuma APC ta bayyana lokacin da shugaba Buhari zai yi Maganin Yan ta'adda da masu ɗaukar nauyinsu
Jam'iyya mai mulki, APC, ta bayyana cewa nan gaba kaɗan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yan majalisarsa zasu kawo ƙarshen rashin tsaron ƙasar nan.
APC ta faɗi haka ne a wani jawabi data fitar ɗauke da sa hannun sakataren ta, John Akpanudoedehe.
Asali: Legit.ng