Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca

Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca

- Wata Mata ma'aikaciyar lafiya a jihar Nasarawa ta bayyana babbar illar da rigakafin korona ta Astrazeneca ta yi mata

- Matar mai suna, Goselle Manya, ta kwanta matsanancin rashin lafiya tun bayan da aka yi mata rigakafin wadda akace wajibi ce ga ma'aikatan lafiya

- Tace tunda aka mata rigakafin tafara ganin jiri amma sai ta ƙoƙarta ta koma gida, daga nan kuma sai ciwon kai

Wata mata yar kimanin shekaru 31 a duniya ta kwanta rashin lafiya mai tsanani tun bayan da akai mata allurar rigakafin Astrazeneca domin kariya daga cutar COVID19 a jihar Nasarawa.

KARANTA ANAN: Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

Matar mai suna, Goselle Manya, tana aikin sa kai ne a asibitin kula da lafiya a matakin farko dake Azuba Bashiyi ƙaramar hukumar Lafiya, jihar Nasarawa.

Rahotanni sun tabbatar da matar ta fara ciwon ne bayan anyi mata rigakafin Astrazeneca, wadda yake wajibi ga ma'aikatan lafiya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yayin da take bayyana abunda ya faru da ita bayan yin rigakafin, Goselle Manya, tace an mata rigakafin ranar 22 ga watan Maris, kuma tun daga lokacin ta fara ganin jiri.

Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca
Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca Hoto: africanews.com
Asali: UGC

A bayanin da tayi, Manya tace:

"Mintuna 15 bayan an mun rigakafin sai nafara ganin jiri, nayi tsammanin matsalar ta lokacin ne kaɗai, amma bayan na koma gida sai na fara ciwon kai. Kuma lafiyata kalau kafin amun allurar."

"Bayan haka na kai korafin abinda ke damuna tun bayan da aka mun allurar a asibitin da nike aiki, amma sai suka cemun zazzaɓin cizon sauro ne, da zarar nasha magani zan warke."

KARANTA ANAN: NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok

"Bayan makwanni uku na gama shan magungunan zazzaɓin cizon sauron, sai kuma na fara ganin wani abu na fitomun a fatar jikina gaba ɗaya ga kuma matsanancin ciwan kai."

Matar ta cigaba da cewa: "Da lamarin ya cigaba, sai wata ma'aikaciyar NAFDAC ta ce inzo ofishinsu a ƙara duba lafiya ta"

"Lokacin da naje can, ma'aikatan wajen sun yi mun wasu tambayoyi, daga baya suka kaini asibitin Dalhatu Arafat, aka kwantar dani na tsawon kwana uku."

"Har yanzun ina kwance, bana iya zuwa aiki, gashi bani da kuɗin gwaje-gwajen da akace nayi a asibiti. Ina cigaba da neman tallafin dazan kula da lafiyata."

A wani labarin kuma Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos

An shiga musayar yawu tsakanin jam'iyya mai Mulki, APC, da kuma babbar abokiyar hamayyarta PDP a jihar Lagos kan adadin mutanen da APC tayiwa rejista.

Shugaban kwamitin yin rijistar APC na jihar Lagos, Dr. Muhammad Bashiru, yace sunyi wa mutane 2.5 miliyan rijistar zama yan jam'iyya a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel