Cikakken Bayani: Yadda jirgin yaƙin NAF da Boko Haram Suka hallaka sojoji 33 a Mainok
- Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji dayawa sun rasa rayukansu a musayar wutar da sukayi da mayaƙan Boko Haram da kuma kuskuren wani jirgin yaƙin NAF
- Jirgin yaƙin dai ya jefa bom ne a kan wata motar yaƙin sojoji waɗanda ke kan hanyarsu na zuwa kai ɗauƙi garin Mainok
- Daraktan yaɗa labarai na rundunar Sojin,.Muhammed Yarima, yace jami'an soji sun aika yan Boko Haram da yawa lahira a wata fafatawa
Aƙalla sojojin Najeriya 33 ne suka rasa rayukansu ranar Lahadi daga cikinsu harda mai riƙe da ofis kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin yaƙin rundunar sojojin sama (NAF) yayi kuskure, inda ya farmaki wasu sojojin ƙasa dake kan hanyarsu ta zuwa garin Mainok.
KARANTA ANAN: Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca
Jirgin dai yayi niyyar maida martani ne ga mayaƙan Boko Haram amma sai aka samu wannan kuskuren wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan sojoji da dama.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wasu mayaƙan Boko Haram da suka yi shiga irin ta soji sun shiga sansanin sojojin dake Mainok, kuma sukayi wa sojojin ɓarna da kayan aikinsu.
Hakanan kuma jirgin yaƙin NAF ya jefa bam a wata motar yaƙi wadda take tare da wasu sojoji a kan hanyar su ta zuwa garin domin su kai ɗauki.
Ana ganin dai harin da yan Boko Haram suka kai garin Mainok yafi kowanne hari Muni a wannan makon sabida irin mummunar ɓarnar da akayi.
Sai-dai a ranar Litinin, NAF tace zata binciki rahoton da ya bayyana cewa mutanenta sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji 20 a wani harin jirgin yaƙi.
Hakanan kuma a wani jawabi da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji yayi, Mohammed Yerima, yace sojoji shida sun rasa rayukansu yayin da aka kashe da yawa daga cikin yan Boko Haram a wani hari da suka kai.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe
Yerima yace:
"Bataliyar sojoji ta 156 ce ta riƙe yan ta'addan har sai da rundunar kawo ɗauki ta ƙariso daga sansanin soji na musamman dake Benesheik."
"A lokacin musayar wuta wanda ya shafe awanni da dama ana yi, jami'an sojin sun yi amfani da dabarunsu wajen aika da yawa daga cikin yan ta'addan zuwa lahira a tsakankanin sansanin sojin."
"Ana cikin haka ne, wani jirgin yaƙi ya ƙaraso wajen inda ya cigaba da kakkaɓe ragowar waɗannan yan ta'addan da sojoji suka ritsa."
"Bayan wannan artabu, sai ga gawarwakin mayaƙan Boko Haram da yawa a wurin, da kuma motocin yaƙin su da aka lalata a yayin fafatawar. Amma labari mara daɗi shine sojoji shida sun rasa rayuwarsu a wannan musayar wutan." inji shi.
A wani labarin kuma Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos
An shiga musayar yawu tsakanin jam'iyya mai Mulki, APC, da kuma babbar abokiyar hamayyarta PDP a jihar Lagos kan adadin mutanen da APC tayiwa rejista.
Shugaban kwamitin yin rijistar APC na jihar Lagos, Dr. Muhammad Bashiru, yace sunyi wa mutane 2.5 miliyan rijistar zama yan jam'iyya a faɗin jihar.
Asali: Legit.ng