'Yan Bindiga Sunyi Ƙoƙarin Afkawa Unguwar Hausawa a Imo

'Yan Bindiga Sunyi Ƙoƙarin Afkawa Unguwar Hausawa a Imo

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi yunkurin kai hari unguwar Hausawa a Imo

- Rahotanni sun ce mazauna unguwar sunyi kwanan zaune saboda karar harbin bindiga da suka rika ji cikin dare

- Hon Suleiman Ibrahim Suleiman, babban mashawarcin Gwamna Hope Uzodinma kan harkokin yan Arewa ya tabbatar da faruwar lamarin

An shiga firgici a layin Douglas da ke Owerri babban birnin jihar Imo a yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suke kokarin afkawa yankin Hausawa da ke unguwar a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yi ta jin karar harbin bindiga a daren ranar Litinin a yayin da sojoji da yan sanda da aka tura unguwar ke fafatawa da yan bindigan.

'Yan Bindiga Sunyi Ƙoƙarin Afkawa Unguwar Hausawa a Imo
'Yan Bindiga Sunyi Ƙoƙarin Afkawa Unguwar Hausawa a Imo. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefawa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure

Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke gudu don kare ransu sakamakon musayar wutar.

An gano cewa yan bindigan sun tafi bayan sun gaza jure luguden wuta da jami'an tsaron ke musu.

Babban mashawarci na musamman ga gwamna Hope Uzodinmma a kan harkokin yan Arewa da marasa galihu, Hon Suleiman Ibrahim Suleiman ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami'an tsaron sun dakile harin da yan bindigan suka kai.

KU KARANTA: 'Yan gudun hijira sunyi zanga-zanga sun tare babban titin Makurdi zuwa Lafia

Ba a yi nasarar ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi, SP Orlando Ikeokwu ba a kan batun.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel