'Yan Gudun Hijira Sunyi Zanga-Zanga Sun Tare Babban Titin Makurdi Zuwa Lafia

'Yan Gudun Hijira Sunyi Zanga-Zanga Sun Tare Babban Titin Makurdi Zuwa Lafia

- Mutane da ke sansanin yan gudun hijira a jihar Benue sunyi zanga-zanga kan kashe wasu mutane a sansanin yan gudun hijira

- Yan gudun hijirar sun rufe titin Makurdi zuwa Lafia don nuna rashin jin dadinsu kan harin da aka kai musu

- Gwamnan jihar Benue, Mr Samuel Ortom ya tafi titin da suke zanga-zangar ya basu hakuri kafin suka bude hanyar

Dururuwan mutanen da suke zaune sansanin yan gudun hijira sun rufe babban titin Makurdi zuwa Lafia kan mutuwar wasu mutane 10 da ake ce makiyaya ne suka kashe a daren ranar Litinin a sansanin, The Nation ta ruwaito.

Sun tare babban titin tare da gawarwakin yan uwansu da aka kashe wanda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a babban titin.

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya tafi wurin da yan gudun hijiran ke zanga-zangar inda ya roke su da su bude hanyar domin motocci su rika wucewa.

Ga hotunan masu zanga-zangar a kasa:

'Yan gudun hijira sunyi zanga-zanga sun tare babban titin Makurdi zuwa Lafia
'Yan gudun hijira sunyi zanga-zanga sun tare babban titin Makurdi zuwa Lafia. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

'Yan gudun hijira sunyi zanga-zanga sun tare babban titin Makurdi zuwa Lafia
'Yan gudun hijira sunyi zanga-zanga sun tare babban titin Makurdi zuwa Lafia. @TheNationNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger

A safiyar ranar Talata ne yan bindigan suka afka cikin sansanin yan gudun hijirar da ke Abagena suka kashe mutane shida.

Sansanin yana kan hanyar Makurdi ne zuwa Lafiya a jihar Benue.

Wasu mutanen da dama sun kuma samu rauni sakamakon harin yayin da mutanen da ke zaune a sansanin suka rika tserewa don tsira da rayukansu.

Zanga-zangar da aka yi ya saka wasu ababen hawa da dama masu zuwa Makurdi sunyi ta juyawa akan tilas suna juyawa saboda rashin tabbas din abin da za su tarar a hanyar.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel