'Yan Bindiga Sun Afkawa Ayarin Motocin Sojoji Sun Kashe Huɗu

'Yan Bindiga Sun Afkawa Ayarin Motocin Sojoji Sun Kashe Huɗu

- Yan bindiga sun kai wa ayarin motoccin sojoji hari a Rivers, sun halaka hudu sun raunata wasu

- Bata garin sun kuma yi awon gaba da ma'aikatan kamfanonin man fetur da sojojin ke yi wa rakiya a Omelema

- Kakakin rundunar yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni ya ce yana da masaniya kan afkuwar harin amma ba shi da cikaken bayani

Sojoji hudu sun mutu yayin da wasu biyu suka samu raunukan harsashi a ranar Litinin a karamar hukumar Abua/Odua a jihar Rivers a yayin da yan bindiga suka afkawa ayarin motoccin ma'aikatan man fetur da sojojin ke yi wa rakiya a karamar hukumar Omelema, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan Bindiga Sun Afkawa Ayarin Motocin Sojoji Sun Kashe Huɗu
'Yan Bindiga Sun Afkawa Ayarin Motocin Sojoji Sun Kashe Huɗu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurɗi

Hakan na zuwa ne bayan wasu da ake zargin yan kungiyar IPOB ne sun kashe jami'an tsaro a Omagwa da Isiokpo da ke karamar hukumar Ikwerre na jihar da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro ciki har da sojoji da yan sanda da kwastam.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa yan bindigan sun afkawa sojojin da ke yi wa ma'aikatan man fetur din rakiya a Omelema a ranar Litinin kafin sace ma'aikatan man fetur din.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

An yi kokarin ji ta bakin Mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, 6 Division da ke Port Harcourt, Manjo Charles Ekeocha amma hakan bai yiwu ba domin bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Da aka tuntube shi, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni ya ce yana da masaniya kan afkuwar harin amma ba shi da cikaken bayani.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164