Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

- Shugaban kwamitin kula da ayyukan sojoji, Sanata Ali Ndume, ya baiwa gwamnatin tarayya muhimmiyar shawara kan yadda yakamata tayi da waɗanda ta kama da tuhumar taimakawa yan Boko Haram

- Sanatan yace bai kamata ana nuƙu-nuƙu a lamarin su ba, kamata yayi a gudanar da binciken su a fili

- Ndume ya ƙara da cewa rashin tsaro a ƙasar nan yakai inda yakai, domin bazai ba kowa shawa'ar zuwa ko ina a cikin Najeriya ba

Shugaban kwamitin dake kula da sojoji a majalisar dattawan ƙasar nan, Sanata Ali Ndume, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin yan kasuwar canji (BDC) da aka kama da zargin taimakawa Boko Haram.

KARANTA ANAN: Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Ndume, wanda ya fito daga jihar Borno ya roƙi gwamnatin ta bayyana cikakken bayanan yan BDC ɗin da aka kama zuwa yanzun kowa ya sansu.

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa gwamnati ta kama wasu daga cikin yan BDC da ake zargin suna turawa mayaƙan Boko Haram kuɗi.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja jiya, Ndume yace:

"Kwanan nan fadar shugaban ƙasa tace yan Najeriya zasu sha mamaki idan ta bayyana bayanan waɗanda suke ɗaukar nauyin yan ta'addan Boko Haram. Ka taɓa tunanin yan kasuwar canji 400 ne suke ɗaukar nauyin Boko Haram?"

"Yanzun da aka kama waɗannan mutanen, me gwamnati ta shirya yi akansu? Har yanzun gwamnatin na ikirarin cewa lamarin su na sirri ne, meye abun sirrantawa game da su?"

"Ya kamata gwamnati ta fito ta bayyana cikakken bayani a kansu, kuma ta gudanar da bincikensu a bayyane, mara laifi a sake shi, wanda kuma aka kama dumu-dumu a hukunta shi yadda yakamata."

Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram
Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanatan ya bada misali da lokacin da aka zarge shi, duk da ba gaskiya bane amma yace an gudanar da binciken ne a bayyane kuma saida aka ɗauki shekaru shida ana bincikensa.

KARANTA ANAN: Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa

"Amma yanzun sai kaga an kama mutane an kullesu, daga nan ba zaka sake jin komai game da su ba. Babu wanda yasan abunda yafaru da mutanen da suka kashe sojoji 11 a jihar Benuwai kwanan nan, da mutanen da suka yanka ɗan sanda a jihar Rivers." inji shi.

Ndume ya ƙara da cewa inda kowanne ɗan Najeriya zaiyi abinda ya kamata kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya tanadar, to da an zauna lafiya.

Da yake martani kan shawarar da Amurka ta baiwa yan ƙasarta game da zuwa Najeriya, Ndume yace:

"Amurka na da damar baiwa yan ƙasarta shawara a kan matsalar tsaro, kamar yadda nima bazan ba mutane shawara su dinga tafiye-tafiye ko ina a cikin Najeriya ba."

A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield

Ƙungiyar gwamnonin arewa sun nuna rashin jin daɗinsu da kisan ɗalibai uku daga cikin ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka sace ranar Talata.

Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ta bakin daraktan yaɗa labaransa ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel