Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos

Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos

- An shiga musayar yawu tsakanin jam'iyya mai Mulki, APC, da kuma babbar abokiyar hamayyarta PDP a jihar Lagos kan adadin mutanen da APC tayiwa rejista

- Shugaban kwamitin yin rijistar APC na jihar Lagos, Dr. Muhammad Bashiru, yace sunyi wa mutane 2.5 miliyan rijistar zama yan jam'iyya a faɗin jihar

- Sai-dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da zancen, inda tace wannan shiryayyen abune da APC tayi don jawo hankalin mutane

An samu ɓarkewar hayaniya a siyasar jihar Lagos bayan Jam'iyya mai mulki APC ta bayyana cewa ta yiwa mutane 2.5 miliyan rijistar jam'iyya a jihar Lagos lokacin da jam'iyyar ta gudanar da yin rijistarta a faɗin ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Boko Haram sun fara kafa tutocin su a wasu sassan Geidam

Shugaban kwamitin yin rijistar APC, Dr. Muhammad Bashiru, shine ya bayyana haka yayin da yake gabatar da bayanin yadda aikin ya gudana ga shuwagabanni.

Bashiru yace kimanin mutane 2.5 miliyan ne aka yiwa rijistar a faɗin kananan hukumomi 20 na jihar kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Amma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, ta bayyana adadin da APC ta faɗa da cewa ƙarya ce kawai.

Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos
Sabuwar Rigima ta ɓarke tsakanin manyan Jam'iyyu biyu APC Da PDP a jihar Lagos Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP a jihar, Taofic Gani, ya bayyana APC da jam'iyyar maƙaryata, yace yanzun mutanen jihar basu son APC.

"Wannan bashi ne karon farko da APC tayi wannan ƙarin ba, kowa yasan ƙarya ce kawai. Sabida haka 2.5 miliyan da suka faɗa karyane da kuma ƙage." inji Gani.

Amma kakakin jam'iyyar APC a jihar Lagos ɗin, Seye Oladejo, yace jam'iyyar su zata tabbatar da maganarta a lokacin zaɓen ƙananan hukumomi dake tafe ranar 24 ga watan Yuli.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

Shugaban ƙungiyar yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, yace shugaba Buhari ne babban wanda baison ganin cigaban Najeriya.

Adebanjo yace ba yadda za'a yi sojoji su ƙaƙabama yan Najeriya wannan kundin tsarin mulkin tun 1966 amma Buhari yaƙi yarda a canza shi kuma yace shi mai kishin ƙasa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262