Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa

Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa

- Dakarun sojin rundunar OPWS a ranar Asabar sun kama Mue Ter Cha, Utambe Azder a jihar Binuwai

- An kama basaraken da miyagun makamai tare da harsasai bayan bincikar fadarsa da sojojin suka yi

- Sun kaiwa wani basarake samame bayan kama makamai da suka yi a fadarsa amma ya tsere

Dakarun sojin hadin guiwa karkashin Operation Whirl Stroke a ranar Asabar sun damke dagacin Cha (Mue Ter Cha) Utambe Adzer dake karamar hukumar Ukum ta jihar Binuwai bayan samun miyagun makamai da harsasai a fadarsa.

An gano cewa dakarun sun samu wasu makamai a fadar dagacin Lumbuv, Teran Kwaghbo a yankin kuma sun yi yunkurin kama shi amma ya tsere.

Wata majiya daga yankin da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da Vanguard cewa dakarun OPWS sun yi aiki ne da wasu bayanan sirri inda suka gano makaman a fadar sarakunan biyu.

KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji

Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa
Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki

"Wurin karfe 10:30 na yammacin ranar Juma'a ne muka ga sojoji suna tunkarar fadar Mue Ter Cha. Daga nan kawai muka ga sojojin sun kama basaraken. Mun ga suna fito da makamai wadanda muka ji daga gidansa aka gani.

"Sun kara da kone bukkar dake fadar wacce aka ce yana ajiye makaman a ciki. Da safiyar Asabar kuwa, dakarun sojin an gansu a yankin Lumbuv inda suka yi yukunrin kama dagacin wanda ya tsere.

"A yanzu haka da nake magana, babu wanda ya san inda sojojin suka kai basaraken," yace.

A wani labari na daban, jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya.

'Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021.

Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel