Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

- Rundunar yan sanda reshen jihar Kwara ta samu nasarar cafke mutane huɗu da ake zargin suna da hannu a kashe wani ango kwanaki kaɗan kafin a ɗaura masa aure

- Mutanen sun yaudari angon zuwa wani daji inda suka kashe shi kuma suka nemi amaryarsa ta biya 12 miliyan kuɗin fansa

- Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka bayyana duk yadda akayi har suka yaudare shi zuwa dajin da suka kashe shi a can

Hukumar yan sanda a jihar Kwara ta damke wasu mutane huɗu da take zargin suna da hannu a kisan Olokose Ojo, ma'aikaci a asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin, kwanaki shida kafin ɗaurin aurensa.

KARANTA ANAN: Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

Ana zargin wani maƙocinsa mai suna Kazeem Muhammad, wanda ya jashi zuwa dajin Patigi da niyyar zai taimaka mishi ya siya shanu uku da za'a yi amfani dasu a wajen taron bikinsa.

A wannan tafiya ne suka kashe shi kuma suka binne gawarshi bayan sun zari kuɗi kimanin 1.2 miliyan daga cikin asusun bankinsa ta hanyar amfani da katin bankinsa.

Sannan suka nemi 12 miliyan kuɗin fansa daga wurin budurwarsa wacce zai aura, Ilori Oluwakemi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Amma daga baya yan sanda sun haƙo gawar tasa daga inda aka binne ta, suka kaita ɗakin ajiyar gawa a asibitin da yake aiki.

Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa
Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yan sandan sun bayyana sunayen ragowar mutane uku da suka kama da hannu a kisan; Mohammed Chatta, Jimoh Abdulateef da kuma Madi Jeremiah.

KARANTA ANAN: Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

Yan sandan sun tabbatar da cewa zasu gurfanar da waɗanda aka kama ɗin a gaban kotu da zarar ma'aikatan sashen shari'a sun dawo daga yajin aiki.

Kakakin yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama ɗin sun amsa laifinsu.

Yace: "Sunyi jawabi da cewa sun yaudareshi zuwa wani ɓangaren dajin Patigi bayan an faɗa masa shanun da ya siya suna can. Amma kafin su ƙarasa suka kashe shi."

"Suka binne gawarsa a wani ɗan ƙaramin kabari bayan sun cire wasu sassan jikinsa."

A wani labarin kuma Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

Mazauna garin Kano sun koka matuƙa da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi duk kuwa da shigowar watan Azumin Ramadan.

Mutane da yawa sunce farashin ƙanƙarar ya ƙaru sama da kashi 100%, domin ƙanƙarar da ake siyarwa N100 kafin azumi yanzun ta koma N250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel