Pantami: Tsohon jakada Campbell ya magantu, ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta baiwa ministan biza
- Wani tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell ya yi martani a kan lamarin Pantami
- Campbell ya bayyana cewa Amurka ta fi damuwa da ayyukan ta'addanci ba tunani ba
- Tsohon wakilin ya kara da cewa ayyuka sun fi nauyi fiye da magana ko kalmomi kawai
John Campbell, wani tsohon jakadan Amurka a Najeriya, ya ce 'yancin fadin albarkacin baki da tunani na cikin tsarin Amurka.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Campbell ya ce gwamnatin Amurka ba za ta iya hana ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali-Pantami bizarta ba, bisa lamari na zargi kawai.
KU KARANTA KUMA: Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Legit.ng ta tattaro cewa yayin da yake mayar da martani ga tattaunawar imel da jaridar The Punch a kan zargin a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, tsohon jakadan ya ce hudubar Pantami da sauran bayanan da ya yi a bainar jama'a ba za su iya zama mizanin sanya shi cikin jerin yan ta'adda ba.
Campbell, wanda ya yi aiki a matsayin jakada a Najeriya a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007, ya ce wani jami’in ofishin jakadancin zai so sanin lokacin da aka yi wa’azin Pantami da sauran bayanan da yayi a cikin jama’a.
KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take
Ya ce:
“Har ila yau, akwai tambaya game da ko yana bayar da fatawar tashin hankali ne, ko kuma afuwar da ya nema watsi ne da abunda ya fadi? Shin yanzu yana cikin ƙungiyar ta'addanci ta duniya? Ko kuma, wasu daga cikin ra'ayoyinsa sun yi daidai da na Osama Bin Laden? Kamar yadda kuka sani, 'yancin faɗar albarkacin baki da tunani na tattare da tsarin Amurka."
A gefe uda, ffadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya yi kalamai a baya yana mai goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.
Bayanin fadar shugaban kasar na kunshe ne a cikin jerin sakwannin da babban mai taimakawa shuaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a Twitter.
Asali: Legit.ng