Na shiga uku: Wanda ya yi wa Ganduje tambaya a kan bidiyon Dala ya na fuskantar barazana

Na shiga uku: Wanda ya yi wa Ganduje tambaya a kan bidiyon Dala ya na fuskantar barazana

- Kabir Dakata ya bayyana cewa wasu mutane su na ta bibiyar sahunsa

- Dakata ya ce rayuwarsa ta na fuskantar babban hadari a halin yanzu

- ‘Dan gwagwarmayan ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Facebook

Kabir Dakata, wani ‘dan gwagwarmaya da ya jefa wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje tambaya a kan batun zargin karbar Dala ya na fuskantar barazana.

Malam Kabir Dakata ya bayyana cewa rayuwarsa ta na fuskantar barazana a halin yanzu. Dakata ya bayyana haka a wata sanarwa da ya yi shafin Facebook.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Dakata ya na cikin manyan ‘yan adawar Mai girma Abdullahi Ganduje.

KU KARANTA: Matar da ta ke rigima da Gwamnatin Ganduje ta shiga wasan buya da Hukuma

Da BBC Hausa ta yi hira da Dr. Abdullahi Ganduje kwanakin baya, Dakata ya tado da zargin da ake yi wa gwamnan na karbar cin hanci wajen bada kwangiloli.

Da yake magana a Facebook, Dakata ya ce ya lura ana bibiyarsa. A cewarsa abin ya fara ne tun a a makon jiya. inda wasu mutane a kan babur su ka rika bin motarsa.

Malam Dakata ya ce lokacin an ci sa’a ba ya cikin motar, sai aka ji na kan babur ya na cewa guda: “motar ce amma ba shi bane”, sai dayan ya ce masa: “mu juya kawai.”

Wannan Bawan Allah ya ce daga baya ya je ofis sai mai gadinsa yake fada masa wani ya zo nemansa, har ya bukaci a fada masa lokacin da yake zuwa aiki.

Na shiga uku: Wanda ya yi wa Ganduje tambaya a kan bidiyon Dala ya na fuskantar barazana
Jawabin Kabiru Dakata Hoto: Facebook/Kabiru Dakata
Asali: Facebook

KU KARANTA: Barazana: Fito da bidiyon Ganduje ya sa Jafar Jafar ya boyewa 'magauta'

Bayan an yi wannan, sai kuma wasu su ka sake zuwa unguwarsu da fuskarsu a rufe, su ka zo wajen masu gadi, su ka fada masu cewa su na so a kira masu shi.

Ganin abubuwan da su ka faru, Dakata ya sanar da Duniya, ya ce zai yi magana da lauyoyinsa.

Darektan na cibiyar CAJA ya nemi jin abin da ya hana hukumar binciken rashin gaskiya a Kano ta binciki bidiyoyin da ake zargi gwamnan da lunkuma cin hanci.

Da yake maida martani, gwamnan ya jaddada cewa sharri aka yi masa, aka yi amfani da fuskarsa domin a bata masa suna ta yadda za a hana shi takara a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel