El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka, ya bada wa'adin kwana 7 ko 'yan kasuwa su rasa kadarorinsu

El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka, ya bada wa'adin kwana 7 ko 'yan kasuwa su rasa kadarorinsu

- Gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa 'yan kasuwar Panteka dake jihar wa'adin kwanaki 7 da su tatattara komatsansu

- A cikin tsarin raya birane da habaka su, gwamnatin zata rushe tsohuwar kasuwar Panteka mai shekaru 60

- Ta bukaci 'yan kasuwan su tashi a cikin lokacin da aka basu ko kuma ta rushe kuma su rasa dukiyoyinsu

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada wa'adin kwana bakwai kacal ga 'yan tsohuwar kasuwan Panteka dake kusa da makarantar foliteknik ta Kaduna, da su tattara komatsansu tare da barin wurin.

Kasuwar ta kasance a wurin kuma tana wanzuwa tun shekaru 60 da suka gabata.

Gwamnatin ta ja kunnen 'yan kasuwan da su tattara su bar ta a cikin kwanaki 7 ko kuma su rasa kadarorinsu.

Hukumar tsari da habaka birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta bada wa'adin kwana bakwai ga mazauna kasuwan fara daga ranar Juma'a da ta gabata.

KU KARANTA: Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki

El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka, ya bada wa'adin kwana 7 ko 'yan kasuwa su rasa kadarorinsu
El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka, ya bada wa'adin kwana 7 ko 'yan kasuwa su rasa kadarorinsu. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

A wata takarda da darakta janar na KASUPDA yasa hannu kuma ya fitar, Isma'ila Dikko, yace "A cikin tsarin gyara birane na gwamnatin jihar Kaduna, an baku wa'adin kwana 7 daga ranar da kuka samu takardar nan da ku tashi tare da kwashe dukkan kayanku daga wurin.

"Rashin biyayya ga wannan umarnin zai sa hukuma ta kwace dukkan kayanku tare da rushe ginin a lokacin da wa'adin ya cika kamar yadda sashi na 60, sakin layi na 2 ya tanadar."

Tun farko dai, jama'a kamar tsohon shugaban makarantar dake makwabtaka da kasuwar, Farfesa Muhammad Idris Bugaje, ya roki gwamnan da kada ya rushe tsohuwar kasuwar, a madadin haka, ya mayar da ita wurin tarihi.

Tsohuwar kasuwar Panteka ta kwashe shekaru inda ta kasance wurin siyar da sassan ababen hawa har da jiragen sama wanda makera ke hadawa.

KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji

A wani labari na daban, kafafen yada labarai dake kasar Chadi sun fitar da rahoto masu karo da juna a kan zargin da ake na jin tashin harsasai a fadar shugaban kasar dake N'Djamena.

An gano cewa takaddama ce ta barke tsakanin iyalan marigayin shugaban kasan da ya kwashe shekaru 30 yana mulkin kasar a kan nadin dansa Mahamat Idriss Deby Itno da aka yi a matsayin magajin mahaifinsa.

A wasu sakonni da Tchadinfos ta fitar a kafar sada zumunta ta Twitter, ta musanta rade-radin da ake yi na harbe-harben da aka yi fadar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel