Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki

Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki

- Wani matashi dan Najeriya ya kawo sabon salon noman zamani wanda ya burge jama'a

- Mutumin mai suna Samuel Ogbole yana noman amfanin gonansa ne a iska ba a kasa ba

- Ma'abota amfani da kafar sada zumuntan zamani sun nuna mamakinsu akan yadda yake noman da kuma yawan amfanin da yake samu

A wannan lokacin da zamanin, matasa a Najeriya suna ta fadawa harkar noma wacce suka mayar da ita sana'a.

Samuel Ogbole matashi ne da ya fada aikin noma da salon da ya zama sabo. Matashin manomin, kamar yadda @NigeriaStories ta ruwaito, yana yin nomansa ne a iska ba a kasa ba kamar kowa.

KU KARANTA: A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki

Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki
Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki. Hoto daga @Nigeriastories
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

A yayin bayyana yadda yake nomansa tare da hotunan, @NigeriaStories tace yana amfani da wani salo da ake kira da "aeroponics".

Wallafar tace: "Samson Ogbole kenan, manomi dan Najeriya dake shuka a kan iska. Yana amfani da wannan salon ne wurin shuka ba tare da ta taba kasa ba kamar yadda aka saba."

Salon aeroponics ana amfani dashi ne wurin shuka ba tare da kasa ba ko ruwa amma a sagale a sama.

Tuni 'yan Najeriya suka fara tsokaci a kan wannan hazaka ta matashin. Wani mai amfani da @ohluhjehrey, cewa yayi: "Kasar shuka a Najeriya ba matsala bace. Wannan kirkira zata yi kyau a jihar Legas. Jinjina!"

@ObinnaChuykwukad cewa yayi: "Kudancin Najerya tana bukatar wannan salon wurin shuka. Zai taimaka wurin rage tsadar abinci tare da samun 'yanci ta yadda arewa ba zasu hana mu abinci ba don mun yi fada."

@TundeUnusual rubuta yayi: "Wannan abun jinjina ne! Amma babu kasa? Me yayi amfani dashi ya zuba a cikin gororin can?"

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Abubakar Suleiman Idris, yace magoya bayan jarumar fina-finai, Rahama Sadaua, makiya Musulunci ne da yankin arewacin kasar nan.

Idris ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Afirilu bayan wani George Onmonya Daniel ya jinjinawa jarumar a kan rabon kayan abinci da tayi ga mabukata.

Kamar yadda Abubakar yace, George da sauran magoya bayan jarumar a kan abinda ta raba duk makiya Musulunci ne da arewa saboda yanayin tsarin rayuwarta babu Musulunci a ciki balle kuma yankin arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng