Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji
- Wani dan Najeriya ya bada labarin yadda yayi wa sirikarsa ciki kuma ta haifa masa da namiji
- Ya sanar da cewa ya sha giya a wurin shakatawa yayin da suka hadu da ita kuma suka sadu har da samun rabo
- Sirikarsa ta bar cikin saboda tana fama da gorin cewa diya mace daya tak ta haifa a duniya, haka yasa tace yaron dan mijinta ne
Wani dan Najeriya ya bar masu amfani da kafar sada zumuntar zamani baki bude bayan ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki kuma ta haifa masa yaro namiji.
Mutumin ya bada bayani dalla-dalla a kan alakar dake tsakanin sirikarsa da shi a wata hira da mai sauraro zai kira na wani shirin gidan talabijin.
Ya ce ya fara sanin sirikarsa ne bayan an saka ranar aurensu da matarshi.
Kamar yadda yace, sun yi kwana daya da ita bayan haduwarsu a wani wurin shakatawa da abokansa.
KU KARANTA: Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga
KU KARANTA: Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki magoya bayan Sadau
Mutumin yace ya bugu a lokacin, kuma ya sha mamaki bayan ta samu ciki kuma ta haife tare da cewa na mijinta ne duk da ya san nashi ne.
Mutumin ya bayyana cewa, ya tambaya sirikarsa dalilinta na haifar yaron, sai tace ta yanke wannan shawarar ne saboda mijinta ya saba yi mata gorin cewa diya mace daya tak ta taba haihuwar masa.
Mutumin ya bayyana bakin cikin da yake ji a duk lokacin da yaga kanin matarsa kuma ya san cewa dan shi ne, The Nation ta wallafa.
Ya bayyana nadamarsa tare da mika bukatar shawara ga masu sauraron shirin.
A wani labari na daban, masarautar Kano ta musanta siyar da filayen Gandun Sarki wadanda yasa hukumar yaki da rashawa ta jihar kano take tuhumar Sarki Aminu Bayero da shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawan tana bincikar masarautar akan zargin siyar da filaye har kadada 22 dake Gandun Sarki a Dorayi Karama ta karamar hukumae Gwale dake jihar Kano tare da waskar da kudin zuwa aljihunsu.
Takardun karar da wani wanda ya siya filin, Alhaji Yusuf Aliyu ya shigar, ta bukaci kotun da ta dakatar da shugaban hukumar daga hana su aikin ginin da suka fara.
Asali: Legit.ng