Labarin Sheke Mahamat Deby da ya karba mulkin Chadi: Menene gaskiyar lamarin?

Labarin Sheke Mahamat Deby da ya karba mulkin Chadi: Menene gaskiyar lamarin?

- Rahotanni sun fara yaduwa na cewa an harbe shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno

- A safiyar Alhamis ne aka tabbatar da cewa an ji harbe-harbe a fadar shugaban kasan wanda aka ce rikici ne tsakanin iyalan marigayi Deby

- Kafar yada labarai ta kasar Chadi ta fito tace Shugaba Mahamat Deby na cikin koshin lafiya kuma basu samu sabani da dan uwansa Zakaria ba

Kafafen yada labarai dake kasar Chadi sun fitar da rahoto masu karo da juna a kan zargin da ake na jin tashin harsasai a fadar shugaban kasar dake N'Djamena.

An gano cewa takaddama ce ta barke tsakanin iyalan marigayin shugaban kasan da ya kwashe shekaru 30 yana mulkin kasar a kan nadin dansa Mahamat Idriss Deby Itno da aka yi a matsayin magajin mahaifinsa.

A wasu sakonni da Tchadinfos ta fitar a kafar sada zumunta ta Twitter, ta musanta rade-radin da ake yi na harbe-harben da aka yi fadar.

KU KARANTA: Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki

Labarin Sheke Mahamat Deby da ya karba mulkin Chadi: Menene gaskiyar lamarin?
Labarin Sheke Mahamat Deby da ya karba mulkin Chadi: Menene gaskiyar lamarin?. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

Amma wata majiya ta tabbatarwa da kafar Toubou cewa tabbas Mahamat Deby ya ji raunika daga harbe-harben da aka yi.

Amma kuma Tchadinfos cewa tayi, "Shugaban kasa na rikon kwarya yana da ran shi kuma cikin koshin lafiya. Ba a samu harbe-harbe ba kuma ba a samu sabani tsakanin Mahamat da dan uwansa Zakaria ba."

Tabbas marigayi Deby yana da 'ya'ya masu tarin yawa domin kuwa yayi aure da yawa. A halin yanzu ba a san yawan 'ya'yansa ba.

Ita kuwa jaridar Alwahida Info ruwaitowa tayi cewa, babu shakka an ji karar harsasai a Ati, wacce ke da nisan kilomita 378, gabas da N'Djamena sakamakon yunkurin da fursunoni suka yi na tserewa.

A halin yanzu kuwa jaridar ta tabbatar da cewa kura ta lafa.

A wani labari na daban, Sunday Erhabor, dan sanda mai mukamin ASP, wanda wani mai abun hawa yaci zarafi a jihar Legas, yace bai taba harbin kowa ba tunda ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1992.

Bidiyon yadda wani mutum da 'yan sandan runduna ta musamman suka tsayar, amma ya ci zarafin 'yan sandan ya fada kafafen sada zumuntar zamani.

An ga direban mai suna Victor Ebhomenyen, yana ture Erhabor, wanda ke dauke da bindiga kirar AK-47, a kirji yayin da yake yunkurin kai shi kasa, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel