Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye

- A yanzu haka ana nan ana gudanar da jana'izar tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby, wanda ya rasu a farkon makon nan

- Shugaba Debby ya rasu ne a yayin fafatawa da mayakan 'yan tawaye

- Shugabannin kasashe da dama sun hallara a wajen jana'izar wanda ake gudanarwa a N'Djamena, babban birnin kasar

A yau Juma'a, 23 a watan Afrilu ne ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby, wanda ya amsa kiran mahaliccinsa a farkon mako sakamakon raunukan da ya samu a lokacin fafatawa da 'yan tawaye.

Shugaba Deby dai ya mutu ne kwana daya bayan sakamakon zabe ya nuna shi a matsayin wanda ya yi nasara inda yake shirin soma mulki a wa'adi na shida. Ya kuma shafe sama da shekaru 30 yana mulkar kasar.

KU KARANTA KUMA: Kwanaki bayan dawowar Buhari daga Burtaniya, Fadar Shugaban Kasa ta sake magana a kan lafiyar shugaban kasar

Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Asali: Getty Images

An kuma bayyana dan marigayin, Mahamat Idriss Déby Itno wanda aka fi sani da Janar Kaka a matsayin wanda zai jagoranci kasar na watanni 18 zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.

Shugabannin kasashe da dama sun hallara a wajen jana'izar wanda ake gudanarwa a N'Djamena, babban birnin kasar.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Hajiya Aishatu, Diyar Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ta rasu

Ga karin hotuna a kasa:

Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Asali: Getty Images

Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Asali: Getty Images

Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Asali: Getty Images

Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Hotunan jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi da ya mutu yayin fafatawa da ‘yan tawaye
Asali: Getty Images

A wani labarin, a ranar Alhamis, Ministan harkar tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya yi magana game da kashe shugaban Chadi, Idriss Deby, da aka yi.

Janar Bashir Magashi ya bayyana cewa kisan Idriss Deby zai iya jawo wa Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da Chadi, matsalolin tsaro.

A dalilin haka gwamnatin tarayya ta ce ta inganta tsaro domin a tabbatar da wanzurwar zaman lafiya, kuma ta na bibiyar kasar da ta ke kan iyakarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel