Kwanaki bayan dawowar Buhari daga Burtaniya, Fadar Shugaban Kasa ta sake magana a kan lafiyar shugaban kasar
- Fadar shugaban kasa ta ce wadanda ke ci gaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari mugun fata ba za su yi nasara ba a makircin su
- Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce hakan martani ne ga ikirarin cewa har yanzu shugaban na rashin lafiya
- Adesina ya bayyana cewa bayan kasancewar shugaba Buhari cikin koshin lafiya, yana da karfin da zai iya yin hira da jama’a tun dawowarsa daga Landon
Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya bayar da amsa ga mutanen da har yanzu suke zargin cewa ubangidan na shi yana cikin yanayi na rashin lafiya.
Adesina a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, ya ce wannan mummunan matsayi da tunanin ya fito ne daga mutanen da ba sa nufin Shugaban kasar da komai face sharri a kowane lokaci.
KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take
A cewar Adesina, ikirarin da ke tsakanin wadannan mutane wadanda har suka kai ga kiransa a kan shakkunsu shi ne cewa tun lokacin da shugaban kasar ya dawo daga kasar Ingila bai bayyana ba a gaban jama'a, suna masu tunanin cewa akwai wani abu da ke damun shi.
Da yake martani ga alamarin, Adesina ya bayyana cewa shugaban na Najeriya yana da karfi har ma ya amsa wata hira a filin jirgin sama, yana mai cewa an duba lafiyarsa cikin nasara.
KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa ya bada gudummawar Naira miliyan 2 ga makarantar soja domin aikin masallaci
Ya yi mamaki:
"To daga ina wannan jita-jitar ta fara a ranar Lahadi? Daga mutane masu zuciyar mugunta, waɗanda ba sa son gani ko jin kowane irin abu na alheri. Sun kasance mutane masu jiran tasowar guguwa a kullun, don haka basa taba jin dadin saukar ruwan sama.
"Tun daga ranar farko a ofis, suka yi wa Shugaban kasa kawanya, amma sai kawai Allah ya mayar da su abun dariya. Wanene mutumin da zai fadi abu kuma ya faru, alhali Allah bai ce haka ba?"
Adesina ya ce irin wadannan mutane marasa tunani sun ki koyar darasi daga kayen da suka sha a kokarinsu na ganin ubangidansa ya durkushe.
A wani labarin, fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya yi kalamai a baya yana mai goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.
Bayanin fadar shugaban kasar na kunshe ne a cikin jerin sakwannin da babban mai taimakawa shuaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a Twitter.
Shehu a cikin jawabin nasa a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, ya kare ministan tare da gabatar da cewa Pantami ya ce akwai kuruciya tare da shi a lokacin da yayi wadannan kalaman.
Asali: Legit.ng