Yanzu-Yanzu: Masu garkuwa sun sace fasinjoji 18 a Ibarapa

Yanzu-Yanzu: Masu garkuwa sun sace fasinjoji 18 a Ibarapa

- Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace fasinjoji 18 a Ibarapa a jihar Oyo

- Wani dan banga a yankin mai suna Olatunji Badmus ya tabbatar da afkuwar lamarin

- An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Adewale Osifeso amma bai amsa wayarsa ba

A sace a kalla matafiya 18 a yankin Igbo-ora da ke Ibarapa a jihar Oyo kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wadanda aka sace din fasinjoji ne da ke cikin motar bas mai daukan mutane 18 da aka ce an yi garkuwa da su tsakanin Igbo-Ora da Eruwa a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Yanzu-Yanzu: Masu garkuwa sun sace fasinjoji 18 a Ibarapa
Yanzu-Yanzu: Masu garkuwa sun sace fasinjoji 18 a Ibarapa
Asali: Original

Duk da cewa babu cikaken bayani game da faruwar lamarin a yanzu, Olatunji Badmus, dan banga a yankin Ibarapa ya ce an sanar da su afkuwar lamarin.

Ya ce ba zai iya tabbatarwa ko an sanar da rundunar yan sanda na Igboora abin da ya faru ba domin ba shi da lambar yan sandan.

DUBA WANNAN: An yi jana'izar Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a Kaduna

Ya ce motar bas din mai daukan mutane 18 tana nan a gefen titi kan hanyar Igboora zuwa Eruwa.

A halin yanzu ba a san sunayen mutanen da ke cikin motar ba.

An yi kokarin tabbatar da afkuwar lamarin daga bakin, Adewale Osifeso, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Oyo amma hakan ya ci tura domin bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon tes da aka aike masa ba.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel