An yi jana'izar Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a Kaduna

An yi jana'izar Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a Kaduna

- An yi jana'izar marigayi Alhaji Aliyu Kwarbai Sarkin Mota, direban Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato

- Sheikh Ahmad Gumi, babban malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna ne ya jagoranci sallar jana'izar Ali Sarkin Mota

- Bayan yi masa sallar, an birne marigayin a makabartar da ke Unguwan Sarkin Musulmi da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa

An yi jana'izar Alhaji Aliyu Kwarbai, Sarkin Mota, direban tsohon firimiyan yankin arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a garin Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Babban malamin addinin musulunci, Dokta Ahmad Gumi ne ya jagorancin sallar jana'izar da aka yi a babban masallacin Sultan Bello da ke Kaduna bayan nan aka birne shi a makabartar Unguwan Sarkin Musulmi.

An yi jana'izar Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a Kaduna
An yi jana'izar Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a Kaduna. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Sarkin Mota, wanda jagora ne a unguwa, ya rasu a ranar Laraba a gidansa da ke Unguwan Sarki a karamar hukumar Kaduna ta Arewa bayan gajeruwar jinya.

Ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 14 da jikoki da dama.

Daya daga cikin matansa, Hajiya Rabi Musa, yayin hirar da aka yi da ita ta bayyana mijinta a matsayin mutum mai gaskiya.

Yar uwan marigayin, Asiya Musa ta ce iyalansu sun rasa babban madogara.

KU KARANTA: Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, wanda ya samu wakilcin Ciroman Zazzau, Alhaji Shehu Tijjani a wurin jana'izar ya yi addu'ar Allah ya gafartawa marigayin ya saka masa da Aljannatul Firdausi.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel