Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu

Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu

- Rundunar yan sanda reshen jihar Edo ta kuɓutar da mutane 26 a jihar waɗanda akayi kokarin safarar su

- Hukumar tace waɗanda ta kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, da kuma matashiya ɗaya, sai kuma iyaye mata su shida

- Kakakin yan sandan yace tuni suka miƙa waɗanda suka kuɓutar ɗin zuwa ma'aikatar kula da harkokin mata domin tantancewa da kuma maida su gidajensu

Rundunar yan sanda a jihar Ondo tare da haɗin gwuiwar jami'an Bijilanti sun kuɓutar da mutane 26 da ake zargin anyo safararsu daga jihohin Ebonyi, Imo, Abia, Anambra da kuma Akwa Ibom.

A jawabin da yan sandan suka fitar ta bakin kakakin hukumar jihar, SP Kontongs Bello, yace mutanen da aka kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, matashiya ɗaya da mata shida.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan

Ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin suna kan hanyar Evbuotubu a Ekenwan, Benin kafin jami'ai su zo su kuɓutar da su kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

A jawabin kakakin yan sandan, ya bayyana Wata mata mai suna Jennifer ce taje har gidajen mata shida da aka kuɓutar ta dakkosu.

Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata shida da ake ƙoƙarin safararsu
Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata shida da ake ƙoƙarin safararsu Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Kakakin yan sandan yace:

"An ɗakko matan ne bayan an yaudaresu cewa gwamnatin Edo tana bada tallafin kuɗi ga iyaye mata da basu ɗaɗe da haihuwa ba, musamman waɗanda suka haifi yan biyu."

"Matan sunce an tilasta musu su rinƙa fita bara suna kawo ma uwar gidansu Jennifer. Matan sun ƙara da cewa wani ɗan ƙaramin goro ake basu su kula da yayansu kuma su cigaba da bara."

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

Bello yayi kira ga mazauna jihar da suyi watsi da wani rahoto da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa yan sandan Edo sun kuɓutar da mata da ƙannan yara daga ma'aikatar ƙera kayan yara a Benin.

Ya bayyana cewa tuni hukumar yan sanda ta miƙa matan da ƙananan yaran data kuɓutar ɗin zuwa ma'aikatar kula da mata ta jihar Edo domin dubasu da kuma maida su gidajensu.

Hakanan kuma, kwamishinan yan sandan jihar, CP Phillip Aliyu Ogbadu, ya roƙi masu amfani da kafafen sada zumunta da su rinƙa tantance asalin labari kafin su yaɗa shi.

A wani labarin kuma Wasu Yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Osun, Sun harbe Mutum uku

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kai hari kauyen Koka dake jihar Osun inda suka harbe mutum uku amma ba'a rasa rai ba ko ɗaya.

Mazauna garin sun tabbatar da kawo harin ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11:30 na dare bayan wasu yan garin sun kwanta bacci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262