Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

- Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed, yace sam basu tattauna kan lamarin dake faruwa da ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani ba a wajen taron majalisar zartarwa

- Har yanzun dai wasu na cigaba da kira ga ministan ya ajiye aikinsa, wasu kuma na ganin wannan bawani abu bane da zaisa ya aje aikin duba da cewa ya fito yayi bayani

- Lai Muhammed yaƙi yarda ya amsa tambayar da aka masa cewa ko gwamnati zata cigaba da tafiya da ministan ko ba haka ba, kawai yace ba'a kawo zancen a wajen taron ba

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed, ya ce yan majalisar zaryarwa basu tattauna a kan lamarin dake faruwa game da ministan sadarwa ba a yayin taron su na ranar Laraba wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

KARANTA ANAN: Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

A yanzun haka ana cigaba da kira ga ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami, ya sauka daga muƙaminsa ko kuma a sallameshi.

Wasu na cigaba da wannan kira ne saboda wasu kalamai da ministan yayi a baya da suka nuna yana goyon bayan wasu ƙungiyoyin ta'addanci a wancan lokacin.

Sai dai har yazuwa yanzun fadar shugaban ƙasa ta yi gum da bakinta kan lamarin kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan da ake ma wannan zargi dai yana ɗaya daga cikin waɗanda Suka halarci taron majalisar wanda yake gudana ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed
Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed Hoto: @bashirAhmad
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

A lokacin da aka tambayi Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, kan zargin yace basu tattauna lamarin ba a wajen taron.

Sai dai yaki yarda ya amsa tamabayar da aka masa cewa ko gwamnatin tarayya ta amince da Pantami ya cigaba da kasancewa a muƙaminsa.

Lai Muhammed ya amsa da cewa:

"Ba zance komai dangane da ko gwamnati ta amince dashi ko bata amince ba. Zan dai iya amsa tambayarku kai tsaye, ba'a tattauna akan lamarin ba a taron majalisar."

A wani labarin kuma Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

Mazauna garin Kano sun koka matuƙa da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi duk kuwa da shigowar watan Azumin Ramadan

Mutane da yawa sunce farashin ƙanƙarar ya ƙaru sama da kashi 100%, domin ƙanƙarar da ake siyarwa N100 kafin azumi yanzun ta koma N250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: